Jarumin masana’antar Kannywood Adam A. Zango a wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, ya bayyana cewar babu wani abin ke damun kwakwalwarsa.
Tunda farko dai an ga jarumin wanda wasu ke kallo da mutum mai auri saki ya yi wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda yake bayyana wasu abubuwa marasa dadi dake faruwa a tsakaninsa da iyalinsa.
“Na kama matata da laifin yin dan malele amma na ci gaba da zaman aure da ita.
“An tura min bidiyon batsa da matata ta yi da kanta akan na biya Naira milyan daya ko a saka a duniya na yi hakuri na ci gaba da zaman aure da ita.
“Na kama matata da cin amanata da dan uwana na yi hakuri na ci gaba da zaman aure da ita.
“Idan na yi musu kazafi Allah Ya tona min asiri tun a duniya.
“Ku fada min maza nawa ne masu imanin da za su iya hakuri kamar yadda na yi?
“Idan kuna bukatar shaidu ku rubuta min witness a comment section”.
DUBA NAN: Saratu Gidado, Jarumar Kannywood Ta Rasu
Hakan ya sa wasu suke ganin jarumin Adam Zango ba ya ciki hayyacinsa a lokacin da yake wadannan jawabai saboda ana ganin cewa abu ne da ya kamata ya sirrinta ganin cewa abu ne wanda ba kowa ya kamata ya sani ba.