Abin da ya kamata ku sani kan wasan Man United da Leeds
Manchester United za ta karbi bakuncin kwantan wasan mako na takwas a gasar Premier League ranar Laraba a Old Trafford.
United tana ta ukun teburi da maki 42, ita kuwa Leeds United, wadda ta kori Jesse Marsch ranar Litinin tana da maki 18 a mataki na 17 a kasan teburi.
Dan wasan United, Casemiro zai fara hukuncin dakatarwa wasa uku, sakamakon jan katin da aka yi masa a karawa da Crystal Palace.
Watakila Marcel Sabitzer ya fara yi wa United karawar, sai dai Scott McTominay da Christian Eriksen da Donny van de Beek da Anthony Martia na jinya.
Michael Skubala ne zai ja ragamar Leeds a matakin rikon kwarya, bayan da ta sallami Jesse Marsch.
Robin Kosch ya kammala hukuncin dakatarwa, sai dai Rodrigo da Adam Forshaw da kuma Stuart Dallas na jinya.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu
Wasa daya Leeds United ta ci United a karawa 17 baya a Premier League, shi ne 1-0 a Elland Road a Satumbar 2002.
Leeds ta yi wasa 17 a Old Trafford ba tare da nasara ba, tun bayan 1-0 da ta ci ranar 23 ga watan Fabrairun 1981.
An zura kwallo 11 a ragar Leeds a wasa biyu baya da ta ziyarci Old Trafford, tun bayan da ta koma buga Premier, inda aka yi mata 6-2 a Disambar 2020 da kuma 5-1 a Agustan 2021.
Manchester United
Manchester United ta hada maki 16 tun bayan da aka koma ci gaba da wasannin Premier League, bayan gasar kofin duniya a Qatar.
United ta yi wasa 13 a gida ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa – tarihin wasa 20 take da shi a jere a gida ba a doke ta ba tsakanin Disambar 2010 zuwa Satumbar 2011 karkashin Sir Alex Ferguson.
Ta yi wasa takwas a bana da kwallo bai shiga ragarta ba, irin bajintar da ta yi kenan a bara.
Marcus Rashford ya ci kwallo 11 a karawa 13 tun bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar.
Rashford ya zura kwallo a wasa biyar na United a Premier a gida, Wayne Rooney ne mai tarihin ci a wasa takwas a gida daga Disambar 2009 zuwa Maris din 2010.
Saura kwalllo daya Bruno Fernandes ya ci na 100 a Premier League.
A wasa biyar a United tun bayan gasar kofin duniya a Qatar, Fernandez ya ci kwallo ko kuma ya bayar an zura a raga a 2023, ya ci uku ya bayar da biyu aka zura a raga.
Leeds United ta yi wasa bakwai ba tare da yin nasara ba a Premier League, kuma wasa biyu ta ci daga 17 baya da ta fafata, mai canjaras biyar aka doke ta karo 10.
Ta kasa cin wasa a karawa tara da ta yi a tsakiyar mako da shan kashi a shida daga ciki.
Kwallo 11 Leeds ta zura a raga a wasa hudu kafin gasar kofin duniya, wadda ta zura shida a raga a wasa shida, bayan da aka ci gaba da Premier League.
Maki biyar kadai Leeds ta samu a wasannin waje, rashin bajintar da ake da ita a bana, irin makin da itama Bournemouth keda shi.
Crysencio Summerville ya ci kwallo uku ya bayar da daya aka zura a raga wasa biyar a Premier League.