A Jiya Ne Aka Yi Bikin Bude Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Karo Na 24 A Birnin Bejin.
A jiya Juma’a ne, aka kaddamar da bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu karo na 24 a filin wasannin motsa jiki na kasar china dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar , kuma Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, kuma shi ne ya sanar da bude gasar.
Shugaban kwamitin gasar Olympics na kasa da kasa Thomas Bach, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da kuma wasu shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, da shugabanni daga kasashe sama da 30 a nahiyar Turai, Asiya, Afirka, Latin Amurka ne suka halarci bikin.
Gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ita ce babbar gasar wasannin motsa jiki da aka gudanar kamar yadda aka tsara a karon farko, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19. ’Yan wasan motsa jiki sama da dubu 3 da suka fito daga kasashe 90 ne za su halarci gasar, kuma, wasannin da za su yi, da kuma lambobin yabo da za a bayar, sun ne mafi yawa da za’a bayar a tarihin gasar Olympics ta lokacin hunturu.