A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Africa tawagogin ‘yan wasa na kasashen Kamaru da Burkina faso sun yi nasarar tsallakewa zuwa wassanin ‘yan takwas.
Mai masaukin baki, Kamaru ta tsallake zuwa wannan mataki ne bayan ta yi kunnen doki da Cape Verde 1-1 a wasan da suka buga da yammacin ranar Litini.
Haka ita ma Burkina Faso ta kai wannan mataki bayan ta yi canjaras da Habasha 1-1.
Habasha ita ce kasa ta farko da aka fara yin waje da ita a hukumance a gasar ta bana.
Za a fara buga wasan zagayen ‘yan takwas a ranar Litinin, 24 ga Janairu.
A wannan Talata, dai akai jerin wasanni har guda hudu da za’a buga :
Malawi zata fafata da Senegal
Sai kuma Zimbabwe da za ta kara da Guinea
Yayin da Gabon da Morocco zasu kece raini
Sai kuma Ghana da Comoross, duka a yau Talata.