Ƙwallon mata: Sweden ta yi waje da Amurka a Kofin Duniya
Tawagar Amurka wadda ke rike da kambu ta fice daga gasar Kofin Duniya ta Mata bayan da Sweden ta doke ta 5-4 a bugun fenariti bayan wasan ya kare babu ci.
Amurka, wacce ta lashe gasa biyu na baya-bayan nan, ta gallabi Sweden a mintuna 120 na wasan amma golan Sweden Zecira Musovic ta yi gagarumin kokari wurin hana ci.
A bugun fenariti, Lina Hurtig ce ta buga wa Sweden na karshe inda sauran kiris golan Amurka Alyssa Naeher ta hana kwallon shiga raga.
Wannan ne karo na farko da Amurka ta kasa kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar Kofin Duniya ta Mata.
Yanzu Sweden za ta kara da Japan a wasan dab da na kusa da karshe ranar Juma’a, 11 ga watan Augusta..