Tawagar Ghana ta yi ban kwana da gasar cin kofin Afirca ta bana, bayan da Comoros ta doke ta 3-2 a wasa na uku a rukuni na uku ranar jiya Talata.
Comoros wadda karon farko ta fara buga wasannin Afcon ta fara cin kwallo ta hannun El Fardou Ben Nabouhane daga nan kuma aka kori kyaftin din Ghana Andre Ayew wanda aka baiwa jan kati.
Daga karshe Mogni ya kara kwallo ta biyu a wasan kuma na uku a minti na 85 da hakan ya sa Ghana ta yi waje a karawar rukuni a karon farko tun bayan 2006.
Wannan sakamakon zai shiga tarihi a gasar kofin Afirca da ake yi a Kamaru, bayan da Comoros wadda ke buga wasan a karon farko ta yi waje da Ghana mai kofi hudu a tarihi.
Comoros wadda take ta 132 a jerin kasashen da ke kan gaba a taka leda a duniya a jadawalin FIFA, tana da damar zuwa zagaye na gaba, bayan da ta hada maki uku a rukuni na uku, wadda ta sha kashi a wasa biyu a jere a cikin rukuni.
Kungiyoyi 12 ne za su kai zagayen gaba kai tsaye, sannan a hada da hudun da suka sami maki mai tsoka don shiga karawa ta gaba a gasar.