Yan bindiga sun kashe mutane akalla 10 a Yammacin Jihar Tillaberi dake Jamhuriyar Nijar sakamakon wani kazamin harin da suka kai kauyen Danga-Zouani da kuma Korombara.
Wani babban jami’in karamar hukumar yankin ya tabbatar da kashe mutanen 10 lokacin da Yan bindiga akan babura suka bude wuta akan jama’a, kuma yace adadin na iya tashi.
Wani zababben wakilin yankin shima ya bayyana cewar adadin ya kai akalla 15 cikin su harda mutane 4 da aka kashe a Danga-Zouani da kuma sama da 10 aka kashe a gonakin su.
Jami’in ya kara da cewa sun samu labarin kona rumbunan abinci da gidajen jama’a da ake zargin Yan bindigar da aikatawa.
Yan bindiga sun kashe mutane sama da 100 a Yankin Tondikiwindi da aka kai harin lokacin da suka kai farmaki a watan Janairu a kauyukan Tchoma Bangou da Zaroumadereye kafin daga bisani suka gudu zuwa cikin kasar Mali.
Kuma a wannan yanki ne aka kashe sojojin Amurka 4 da na Nijar 5 a wani hari na daban a shekarar 2017.
Alkaluma sun nuna cewar ko a watan Maris wadannan Yan bindigar sun kashe mutane 66 da kona motoci da kuma shagunan aje kayan abinci.
Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen Yankin Sahel dake fama da hare haren Yan ta’adda.
Kasashen yammacin afirka dai suna fama matsanancin rashin tsaro sakamakon kutsen kasashen yammacin turai a nahiyar wanda hakan ya zama babbar barazana ga rayuwar mazauna yankin na yammacin afirka, matsalar da zuwa yanzu aka kasa maganin ta.
Kasashe irin su najeriya, chadi, togo da dai sauran su suna cikin jerin kasashen da makamanciyar wannan matsalar take addaba wacce aka alakanta ta da kasashen yammacin turai da suke ruruta wutar wannan fitina wacce take ta cin rayukan al’ummar wannan nahiya ta yammacin afirka.
Tasirin kungiyoyin wahabiyanci na cikin manyan matsalolin da ake lissafi cikin dalilan wannan matsaloli na tsaro.