‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane biyu daga gidajensu da ke Byazhin, wani yanki da ke kusa da Babban Birnin Tarayya (FCT).
‘Yan bindigar wadanda suka afka wa tsaunin da ke kusa da gidan Lottery da kuma ‘yan mituna kadan daga cocin Libing Faith da ke Byazhin a Kubwa, sun sace wani mutum mai suna Mista Ayodele Somorin kafin su tafi da makwabcin nasa, Mista Oladimeji Josiah.
Wani mazaunin garin, wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Segun, ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), a ranar Laraba. Ya ce mutanen, wadanda aka sace kimanin kwanaki biyar da suka gabata, har yanzu suna wurin da masu garkuwar suke.
“A makon da ya gabata Juma’a, ‘yan bindigar sun kasance a wannan yankin da misalin karfe 11:45 na dare. Ko da yake na je wa’azin coci, matata da ‘ya’ana suna gida. “Matata ta fada a baya kafin harin, ta ga mutane biyu a kusa da gidan makwabta ta taga amma ta yi tsammanin su mazauna ne wadanda ke kokarin adana ruwan sama saboda ya kwana a daren.
“Amma, bayan sun shiga gida na farko suka tafi da Somorin, sai suka tafi gida na biyu inda suka yi ta harbi ba kakkautawa kafin su sace Mista Josiah. Segun ya ce “Lokacin da suka shiga gida na uku, abin takaici a gare su, babu kowa a gida amma sun birkita komai a gidan.”
Ya ce duk da cewa masu garkuwar ba su shiga gidansa ba, har yanzu matarsa ba ta murmure ba saboda firgicin daya daga cikin harsanshin ya shiga gidansa ta daya daga tagoginsa. “Na gode wa Allah babu wanda harsashi ya same shi,” in ji shi.
Ya ce ‘yan bindigar dauke da makamin sun nemi a ba su Naira miliyan 10 kudin fansa kowannensu don sakin wadanda aka sace.
Lokacin da Kamfanin Dillacin Labarai na NAN ya ziyarci iyalan mamatan, matansu, a tattaunawa daban-daban, sun ba da labarin abin da ya faru da su.
Ga bictoria, Somorife, ranar Juma’ar da ta gabata ta kasance ranar tunawa. “Mun riga mun yi bacci lokacin da suka zo. Mun farka lokacin da ‘yan bindigar suka fara buga kofar shiga, suna ihu: ‘Bude kofar. ‘
“Muka kulle kanmu a cikin bandaki tare da yara. Lokacin da suka samu damar shigowa sai suka tinkaro bandakin kai tsaye suka karya kofar sannan suka umarce mu da mu fito daga ciki mu dawo falo mu zauna gaba dayanmu. Su bakwai suna dauke da bindigu a hannunsu, yayin da saura suka tsaya waje basu shigo ba suka haska fitilu masu haske, sun ce basu zo don su cutar da mu ba,” in ji ta.
Bictoria ta ce ‘yan bindigar sun yi wa gidan dirar mikiya, inda suka yi awon gaba da kudadensu, laptop, wayoyi, takalmi, mayukan jiki da kayan abinci. “Daga nan aka umarci mijina ya sanya takalminsa suka tafi da shi,” in ji ta.
Ta ce jikinta ya yi sanyi lokacin da ta fara jin harbe-harbe daga gidan makwabciyarta. bictoria ta ce an kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Byazhin washegari Asabar 22 ga Mayu, kuma jami’an‘ yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru.
” ‘Yan sanda sun gaya mana cewa an sace mazajenmu kuma za su kira mu,” in ji ta. Ta ce masu satar mutanen, wadanda tun a lokacin suke tattaunawa da su, da farko sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan 10. A nata bangaren, Oyinlola, matar Josiah ta ce ba ta da masaniyar cewa mutanen da ke dauke da makamin suna cikin kewayen har sai da suka fara fasa kofar karfe ta barauniyar hanya zuwa dakin zamansu, suna harbin kan mai uwa da wabi.
“Mijina ya ce ni da ‘ya’yana mu je mu buya a bayan gida. Lokacin da suka shigo da karfi, sai suka fara dukan mijina, suna ihu: ‘Ina yaro.’ “Ba su zo bayan gida ba duk da cewa an bude kofar. Daga nan suka tafi da mijina.
“Sun kuma tafi tare da wasu kudi, wayoyi nawa guda biyu, daya daga cikin wayoyin ‘ya’yana, jakankunansu na makaranta, burodi biyu da na saya na Naira 500 kowanne, kayan sawa, da sauransu, kafin su tafi gida na uku inda ba su hadu da kowa ba,” in ji ta. .
Ta ce duk da cewa sun bukaci a ba su Naira miliyan 10 a kan kowane mutum da suka sace a farko, amma sun saukar da shi zuwa Naira miliyan 5 ga kowanne kafin su nemi su biya Naira miliyan daya fansa.
Oyinlola, wanda ya ce akalla harsasai 10 aka tsinta a kasa bayan maharan sun tafi, ya karfafa kalaman bictoria cewa an kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Byazhin.
Uwar mai yara uku ta yi addu’ar Allah ya dawo da mijinta lafiya.
Lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ziyarci ofishin ‘yan sanda na Byazhin, jami’in ‘yan sanda na yanki (DPO), Suleiman Yakubu, ya ce ba shi da sukunin da zai yi magana da dan jarida kan irin wadannan batutuwa, amma za su iya tuntubar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, FCT “in ji shi.
Amma, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Mariam Yusuf, ta tabbatar wa da NAN faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho. Ta ce ‘yan sanda sun fara aiki tare da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
“Mun kaddamar da wani shiri mai muhimmanci don ceton wadanda abin ya shafa daga hannun ‘yan bindigar ba tare da rauni ba kuma muna bin wadanda ake zargi,” in ji Yusuf.