Yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila sun bindige wani matashin bafalasdine har lahira bisa zargin sa da dabawa wani bayahude wuka, yayin da rikice rikice suka kara tsananta a yankin zirin gaza da west bank a gabatowar wata mai alfarma na ramadana.
Kafofin yada labaran Isra’ila kuma sun bayyana cewa wani batahude ya samu raunuka a ranar alhamis a kauyen Gush Etzion dake yankin gundumar kudancin birinin Bethlehem, wanda na daga cikin yankunan da yahudawan suka mamaye.
Rahoton ya cigaba da cewa masu dauke da makamai a falasdinu sun hallaka mutumin, kafin daga baya majoyiyin falasdinawa su tabbatar da cewa sojojin Isra’ila ne suka kashe wani bafalasdine wanda hakan ya haddasa asalin rigimar.
Kafar yada labarai Palestinian news agency Wafa ta tabbatar da cewa wanda aka kashe din sunan sa Nidal Juma’a Ja’afra wanda ke zaune a kauyen Tarqoumya near al-Khalil a kudancin yankin west bank.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan an harbe wasu matasan falasdinawa guda biyu a yayin da suke kokarin kare kansu daga hannun sojojin falasdinawa a yankin ‘yan gudun hijira na Jenin dake arewacin west bank.
Wata majiya daga falasdinun wacce ta bukaci a boye a boye sunan ta ta bayyana cewa lamarin rikice rikicen ya samo asali ne sakamakon rundunar yahudawan sahayoyinya da aka fi sani da elite Duvdevan ne suka fito a daruruwa suna farautar wadanda suka kira da masu laifi a yankunan masu gudun hijira wanda hakan ya harzuka falasdinawa.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa mazauna yankin sun tunkari sojojin, inda su kuma sojojin suka fara harba harsashi mai rai da kuma barkonon tsohuwa a kan falasdinawan.
A wani rahoton kuma daga ma’aikatar lafiya ta falasdinu ya tabbatar da cewa yahudawan sahayoniya sun kashe falasdinawa biyu a yankin Jenin camp yayin da suka kai wani harin ba sani ba sabo a kan raunanan falasdinawan