Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi wa Kungiyar Tarayyar Turai (EU) wankin babban bargo kan rahoton zaben shugaban kasa na 2023.
Ya ce rahoton bai bayar da hakikanin gaskiyar zaben da aka gudanar a kasar ba, amma ya haifar da mummunar fahimta a zukatan al’umma musamman a Jihar Ribas.
Wike ya nuna rashin jin dadinsa ne a lokacin da jakadan EU a NIjeriya, Samuela Isopi, ya kai masa ziyarar aiki a ofishinsa.
Ministan ya ce ya kamata Kungiyar EU ta kasance mai sa ido a zaben da ya gabata ba wai ta gabatar da wani rahoto da ba zai bayar da hakikanin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya ba.
Tawagar masu sa ido a zaben na Kungiyar Tarayyar Turai (EUOM) ta bakin babban jami’inta, Barry Andres, a watan Yuni sun gabatar da rahotonsu na zaben Nijeriya da ya gabata, tare da bayyana wasu muhimman abubuwa guda shida da suka ba da shawarwari a kai.
Wike, ya ce dokokin Nijeriya ba za su iya zama daidai da na EU ba saboda suna da yanayi daban-daban.
Ya ce: “Ban yarda da Tarayyar Turai kan rahoton zaben Nijeriya ba. Ya kamata su kasance masu saka ido ne. Dokokin Nijeriya ba za su iya zama daidai da dokokin EU ba saboda suna da yanayi mabambanta.
“A Jihar Ribas, rahoton EU ya bambanta da abin da ya faru a can. Ta yaya za a iya kwatanta mutanen da suka yi imani da dimokuradiyya kuma suke aiki da ita a matsayin mutanen da ba su fahimci dimokuradiyya ba?
“Damuwarmu ita ce yadda za mu inganta tattalin arzikin kasa, dole ne mu hada kai tare da cimma matsaya kan fannonin ci gaba a Babban Birnin Tarayya da ma kasar baki daya.”
Da take mayar da martani, jakadiyar Tarayyar Turai a Nijeriya, Samuela Isopi, ta ce masu sa ido masu zaman kansu ne suka hada rahoton kuma ba shi da alaka da ayyukanta.
Ta yi alkawarin yin aiki tare da ministan don bunkasa ci gaba a yankin Abuja da ma kasar gaba daya.
Source LEADERSHIPHAUSA