Ana tsaka da kamfen, wata tsagerar mata tayi caraf da mazantakar ‘dan takarar shugabancin kasa na kasar Kenya.
Kamar yadda bidiyon da ya yadu ya nuna, jami’an dake tsaronsa sun yi gaggawar make hannun matar sakamakon yadda ‘dan takarar ya firgice Daga bisani ya mayar da lamarin na nishadi inda yake cewa ita kuma wannan har da damko al’aurarsa.
Bidiyon Farfesa George Wajackoyah, ‘dan takarar kujerar shugabannin kasa karkashin jam’iyyar Roots, yana fuskantar cin zarafi yayin da yake kamfen din darewa kujerar shugabancin kasa.
Jaridun kasar sun rahoto yadda lamarin ya faru inda suka ce ‘dan takarar shugaban kasan Kenyan ya fuskanci tururuwar jama’a yayin da yake kamfen din sa a bayan wata akori kura.
Dan takarar shugaban kasan yana tsaka da bayyana jerin abubuwan da zai yi wa kasar ne lokacin da matar ta shigo cikin jama’a tare da yin caraf da mazakutarsa, lamarin da yasa yayi martanin gaggawa.
‘Dan takarar shugaban kasan ya daka tsalle yayin da jami’an tsaron dake biye da shi suka gaggauta daukar mataki, lamarin da yasa matar ta janye hannunta da gaggawa.
“Kada ki taba ni,” Wajackoyah yace cike da dacin zuciya bayan matar ta yi caraf da mazakutarsa.
‘Dan siyasan ya cigaba da walwalarsa har da wasa da dariya sakanni kadan bayan matar ta janye hannunta daga gabansa.
“Toh, yanzu wannan mazakuta ta ta kama,” Wajackoyah ya sanar da jama’ar yayin da yake dariya.
A wani labari na daban, wata amarya da angonta da suka rasa rayukansu shekaru 30 da suka gabata sun yi aure a wani gagarumin bikin kece-raini wanda ya samu halartar ‘yan uwansu da abokan arziki a Indiya.
Wani ma’abocin amfani da Twitter ‘dan kasar Indiya mai suna @anny_arun ne ya bada labarin yadda auren ya kasance.
Ya yi bayanin cewa, a al’adarsu idan mutum ya mutu yana karami, iyalan mamacin na iya nemo wani wanda ya rasu yana karami ta yadda za a yi musu aure.
Ya kara da cewa, hakan ake yi wa jinjirai da suka mutu yayin haihuwa.
Iyayen jariran mace da namiji sai su amince kuma su aurawa ‘ya’yansu matattun juna idan sun girma.