Tura fah takai bango,Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan matsalar tsaro a arewa maso yammacin ƙasar musamman hare-haren ɓarayin daji da ke kashe mutane da satar mutane.
Yawanci ƴan Najeriyar na nuna fushi ne kan mutanen da ƴan ‘yan bindiga suka ƙona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-ɓauna a yankin jihar Sokoto.
Fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni https://nigeria21.com/hauda ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar hare-haren ‘yan bindiga a yankin nasu.
Wannan ne ya sa ƙungiyar ci gaban al’ummar Gobirawan Najeriya ta rubuta wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari buɗaɗɗiyar wasiƙa tana neman ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a arewacin kasar wanda ya ƙara jan hankalin ƴan Najeriya.
Wasiƙar ta nuna damuwa kan kashe-kashen mutanen da ake yi ba tare da daukar mataki ba – musamman a kananan hukumomin Sabon Birni da Goronyo da Isa da kuma Shinkafi da ke jihohin Sokoto da Zamfara, inda suka ce ƴan bindiga sun zama tamkar wata gwamnti, ta yadda suke cire shugabannin al’umma su naɗa nasu.
Wannan al’amari ya tayar da hankalin ƴan Najeriya inda Sokoto ke cikin batutuwan da ƴan ƙasar suka fi tattaunawa a shafin Twitter har aka ambaci jihar sau fiye da dubu 14 a lokacin rubuta wannan labari a ranar Alhamis.
Yawancin ƴan Najeriya na bayyana alhini ne da kuma takaicin ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga duk da matakan da hukumomi ke iƙirarin suka ɗauka.
Yusuf Anka ankaboy ɗan Najeriya da ke yankin Zamfara ya wallafa a shafinsa na Twitter hotunan lokacin da ake ƙoƙarin binnen gawarwakin mutanen da ƴan bindiga suka ƙona inda ya ce “fasinja 42 aka kone cikin motar bas a Gidan Bawa na jihar Sokoto.
Haka ma batun na ci gaba da jan hankalin masu amfani da Facebook inda labarin harin Sokoto ya razana mutane da dama tare da yi wa mamatan addu’a da kuma neman Allah Ya kawo ƙarshen matsalar ƴan
Kakakin rundunar ‘yan sandan jhar, Sanusi Abubakar, ya ce “mutum 19 ne suka mutu nan take yayin da mutum biyu suka mutu a asibiti.”
Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda suka jikkata suna asibiti ana yi musu magani.
“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.
Wani ganau ya gaya wa BBC cewa: “Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.
“Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa akwai tsirarun mutane daga cikinsu da suka tsira.
Shi ma wani shaidan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce “mutum 45 ne a cikin motar, amma bakwai ne suka tsira da rayukansu, su ma a yanzu haka suna cikin halin ha’ula’i.
“Babu maganar ma ka ga gawa a kammale, sai dai muka dinga haɗa ƙafafu da hannaye daban-daban aka yi musu jana’iza a tare.”
Ya ce shi yana tsaye a tasha ma lokacin da motar ta tashi. “Ƴan Union ne ma na tasha suka gaya mana adadin mutanen da motar ta tashi da su,” a cewarsa.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, sai dai ba a cika samun labarin kona mutane ba.