Unguwar Masanawa a tarihin birnin katsina shahararriya ce, domin kuwa ko ba komai saboda a nan ne manyan waliyai masu karamomi suka rayu a karni na goma sha bakwai. Wadannan waliyai su ne; Wali Danmarina da kuma Wali Danmasani.
An ce cikakken sunan wali Danmarina shi ne, Muhammad Ibn al-Sabbagh. Mahaifinsa Balarabe ne wanda ya taso daga gabashi ya kuma sauka a Katsina, gidan wani malami kuma attajirin marini mai suna Kayaba. Wannan marini an ce, shi ne yake yi wa Sarkin Katsina na lokacin Mamuda da iyalinsa rinin tufafinsu.
Ana nan sai wata rana mahaifin wali Danmarina ya ga ‘yar Sarki Mamudu mai suna Baraka, ya ji kuma yana sonta. Don haka sai ya nemi aurenta, sai kuwa aka kuma aura masa ita akan sadaki zinare shidda. Suka tare a gidan kayaba.
Bayan kimanin wata biyu sai Mallam Muhammadu mahaifin wali ɗan marina ya tashi izuwa gabas, ya bar Baraka da cikin wali dan Marina. Ita kuwa sai Allah yayi mata rasuwa kafin ta haihu, sai kuwa akaje aka binne ta a haka a kusa da wata bishiyar Marina.
Allah da ikonsa, sai ya Ƙadarta aka haifi Wali Ɗan Marina a cikin kabarin nan na kusa da marina yana shan maman mahaifiyarsa a kabarin.
A haka har ya girma. Sai ya kasance yana fitowa lokaci lokaci yana yin wasa da dagwalon tukwanen baba, har wata rana mutane suka faki idonsa aka ɗauke shi zuwa riko wurin Wali Dan Masani, mai suna Mallam Abduljalil.
Ance Wali dan Marina anan ya girma a inda ya nuna karamomi masu ban mamaki. A ciki akwai karamar karatun alkur’ani mai girma, inda ya kasance yana shan Kan malaminsa tun kafin a koya masa. Akwai kuma wata takaddama data tashi a gari game da watan azumin Ramadana, wasu suna cewa watan ya kare, sai aje a duba watan Sallah, wasu kuwa na cewa bai ƙare ba sai washegari.
To, da aka taru sai ba a ga wata ya tsaya ba. Sai Wali dan Marina ya fere fasasshiyar kwarya, yayi mata siffar wata, sannan ya jefa sama. Sai kuwa ta tsaya, ya nunawa mutane yace ga wata can. Sai kowa ya yarda wata ya tsaya.
To shikuma Wali Dan Masani sai ya musanta, yace wannan ba wata bane. Sai Yayi addua, ya mika hannu sama, sai gashi ya riko watan. Ya nunawa mutane, suka kuma yadda. Wannan ita ce takaddamar da ta shiga tsakanin waliyyai biyu, suka nunawa mutane karama.
Tarihin Tarihin