Ana raɗe-raɗin wani rikicin cikin gida na shirin ɓarkewa a jam’iyyar PDP Kwankwasiyya, tsakanin manyan jiga-jiganta biyu.
Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida, tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, kuma ɗan takarar Gwamnan jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019.
Sai kuma Dr. Adamu Yunusa Ɗangwani tsohon Kwamishinan ruwa, kuma tsohon shugaban maa’aikatan fadar Gwamnatin Kano.
Dambarwa ba ta rasa nasaba da kiraye-kirayen da magoya bayan Ɗangwanin ke yi na ya fito takarar Gwamna, abin da kuma bai yiwa masu bin Abba Kabir daɗi ba.
Me ke faruwa a tsakanin ɓanagrorin biyu?
Rahotannin da Freedom Radio ta tattara sun nuna cewa, tsamin dangantakarsu ta soma fitowa fili ne a ranar Alhami 2 ga watan Disambar da muke ciki.
A lokacin da tawagar magoya bayan Sanata Kwankwaso suka taro shi daga filin jirgin sama, sannan suka wuce ta’aziyya gidan Alhaji Yusuf Fantiya, da kuma gidan marigayi Alhaji Sani Buhari Daura.
Sai dai bayan da aka dawo gidan tsohon Gwamnan da ke Miller Road, an zargi wasu magoya bayan Abba Gida-gida da yiwa Ɗangwani ihun “Kano Sai Abba”.
Washegari Jumu’a 3 ga watan, sai ba a ga Ɗangwani ya bi tawagar Sanata Kwankwaso ta zuwa garin Ɗanbatta domin jana’izar marigayi Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan.
Maimakon hakan shi ma tawagarsa daban ta je ta yi ta’aziyya a Ɗanbatta.
A ranar Talata 7 ga watan Disambar dai Dr. Ɗangwani da tsohon Kwamishinan kuɗi Yusuf Bello Ɗanbatta da kuma tsohon ɗan majalisar tarayya Abubakar Nuhu Ɗanburan suka gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.
A cikin wannan hoto da aka yaɗa, ya nuna Ɗangwani baya sanye da jar hula, abin da ba a saba gani ba.