Kungiyar lauyoyin Nijeriya, NBA reshen Ikeja ta bai wa Gwamnatin Tarayya da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos wa’adin kwanaki bakwai da su janye karin kudin wutar lantarki ko kuma su fuskanci tsatstsaurar shari’a.
Shugaban kungiyar reshen jihar, Seyi Olawunmi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Legas.
Olawunmi ya bayyana karin kudin wutar lantarki da kusan kashi 300 cikin 100 da cewa ba kawai rashin tunani ba ne har ma da rashin hankali.
Ya ce, umurnin da hukumar kula da wutar lantarki ta kasa, NERC ta bayar kan batun karin kudin wutar, sam babu lura da yanayin tattalin arzikin talakawan Nijeriya a halin yanzu ba.
Ya ce, reshen zai yi duk abinda da ya dace a gaban kotu idan har gwamnatin tarayya da wadanda abin ya shafa suka gaza janye sabon kudin wutar lantarkin da suka bayyana cikin kwanaki bakwai.
A wani labarin na daban wasu dillalan gidaje a Hotoro (GRA) a jihar Kano sun danganta tashin farashin fili a yankin da kafuwar jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) da ke Kwanar Maggi a yankin.
Daya daga cikin dillalan a yankin, Muhammad Najume, ya shaida wa wakilinmu cewa, tashin farashin ya fara ne nan take bayan da aka fara gudanar da harkokin karatu a jami’ar.
Najume ya bayyana cewa, filin da aka sayar da shi kan Naira miliyan 20 a shekarar 2023 a yanzu ana sayar da shi a kan kusan Naira miliyan 150 ko sama da haka.
“Wannan za a iya danganta shi da yanayin tattalin arziki da kasancewar jami’ar a yankin.
Ya kara da cewa, “Tashin farashin ba wai kawai ya shafi yankin Hotoro ba ne, har ya kai ga makwabtan yankin”.
DUBA NAN: Masu Binciken Tsohon Gwamnan Kano Ganduje Sun Fara Zama
Wani Dillali, Mallam Isa, ya kara bayyana cewa, gidan da bai wuce Naira 500,000 a cikin shekaru uku da suka gabata ba, yanzu ya kai kusan Naira Miliyan 3.