Kungiyar Miyetti Allah ta Fulani ta Maka gwamnan Edo Ortom a Kotu bisa zarginsa da kwace wuraren yin kiwo guda 25,000 mallakar ‘ya’yan kungiyar.
Miyetti Allah ta bukaci kotun ta ICC da ta kawo dauki kan cigaba da tsare fulani makiyaya guda 4,000 da Gwamnatin jihar tayi, kan zargin cewa sun taka dokar haramta yin kiwo a fili da Gwamnatin jihar ta kafa.
Sakatare Janar na kungiyar ta kasa Saleh Alhassan ne ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai.
Alhassan ya ce, kungiyar ta Miyetti Allah ta kai karar gwamnan Ortom ne a gaban kotun ta ICC bisa kwace wa ‘ya’yan kungiyar wuraren yin kiwo a jihar har guda 25,000 sannan kuma ya bayar da umarnin garkame fulani makiyaya har 4,000.
A cewar Alhassan, Ortom na zuwa iyakokin da ke makwabtaka da Benuwai da Taraba ya na kwace shanun Fulani makiyaya inda hakan ke jefa rayuwar ‘ya’yan kungiyar a cikin halin kuncin rayuwa.
Sakamakon rikice rikicen kabilanci gami da rashin tsaro a Najeriya Fulani wadanda suke da al’adar yawo daga wannan wuri zuwa wancan domin kiwon shanun su na cikin babbar barazana.
Ko a wannan satin ance gwamnati na barazanar korar Fulani daga jihar Edo a halin da a kwai haifaffun jihar Edo din cikin fulanin kuma har a kwai ‘yan shekaru hamsin wadanda a ka haife su a Edo.
Fulani suna da hakuri gami da juriyar amma sana’ar kiwo ita suka sa a gaba saboda hakanan ba zasuji dadi ba idan aka gurgunta musu wannan sana’ar da suka gada kaka da kakanni tun zamanin shehi Dan fodio, Inji wani bafulatani da muka samu zantawa dashi.
Ana sa ran hukumomin da abin ya shafe su shiga lamarin domin cero kabilar Fulani mai asali daga wannan balahira.
Source: Leadership