Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wani Matashi masi suna Mohammed Damina wanda aka fi sani da Galadiman Dass kan kisan mahaifin budurwarsa.
An gano cewa Galadima ya fada son Khadija amma yana ta so su fita shakatawa wanda ta sanar da mahaifinta kuma ya bi ta a baya yayin da zasu hadu da shi.
Sai dai cike da rashin sa’a, Khadija ta shigar motar Galadima yayin da mahaifinta ya tsayar dasu, matashin ya ja motarsa inda ya fadi yace ga garin ku.
Ana zargin wannan matashi da halaka tsohon mai shekaru sittin da takwas saboda yana son diyarsa a Yelwa Lebra a daren Lahadi.
Kamar yadda jawabin diyar mai suna Khadija Adamu Babanta ya bayyana, wanda ake zargin mai suna Galadima Dass ya samu lambarta ne daga abokinsa wanda yake ta son ya gan ta amma ta ki, jaridar Vanguard ta rahoto.
“Jiya da yammaci, Galadima ya kira ni yayin da nake shago. Na sanar da iyayena tun farko kuma mahaifina yace a duk lokacin da ya kira in fada masa.”
Galadima ya sake kira kuma nace ya same ni wuraren kasuwar Yelwa Tundu, sai na sanar da mahaifina.
“Ina a daidaita sahu yayin da mahaifina yake babur, a lokacin da muka kai sai yace in shiga motarsa.
Sai nace ya kira, amma sai mahaifina yayi kokarin kama shi yayin da yake ja na zuwa motarsa.
“Ya so tserewa da ni kafin in fito daga motar.
Yayi tukin ganganci yayin da hannayen mahaifina ke cikin motarsa yana kokarin kashe injin.
Daga nan ya buga shi da fol din wuta kuma ya mutu a take.” – Yace.
Khadija tace Galadima ya tsere yayin da gawar mahaifinta ke kwance a kan titi.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili yace: “Jiya wurin karfe 7:30 na dare mun samu labarin mummunan hatsarin mota daga caji ofis din Yelwa don yin bincike.
Mun gano cewa kisan kai ne. “Wata Khadija Adamu Babanta ta hadu da Mohammed Damina wanda aka fi sani da Galadiman Dass.
Lokacin da Galadima ya nuna yana son ta sai ta sanar da mahaifinta abinda ke faruwa kuma tace yana jiran ta a gidan mai.
“Mahaifinta ya bi bayanta har zuwa wurin. Bayan isarsu, mahaifinta wanda yanzu ya rasu, ya yi wa Galadima magana ta bangaren fasinja.
“A yayin da suke magana, Matashi Galadima ya ja motarsa duk da yana wurin tagar motar wanda hakan yasa ya fadi kuma aka kai shi ATBUTH inda aka tabbatar da mutuwarsa. “
Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sanda Umar Sanda ya umarci dukkan kwamandojin yankin da DPO da su hallara a wurin.
Wanda ake zargin yanzu yana hannun ‘yan sanda domin bincike.”
Source:legithausang