Ministan harkokin wajen rasha Sergei Lavrov ya isa kasar chana a yayin ziyarar sa ta farko zuwa wata kasar yankin asiya tun bayan da rashan ta kaddamar da yaki kan kasar ukraine watan daya gabata.
Kamar yadda embassy ta rasaha ta wallafa a shafin ta na sada zumunta ta tabbatar da cewa ministan harkokin wajen na rasha ya isa kasar ta chana, kuma ya sauka a gabashin garin Huangshan, kuma an nuno shi yana ganawa da ma’aikatan lafiya a garin.
Lavrov dai na shirin halartar taron kasashen dake makotaka da kasar afghanisatan a garin Tunxi dake gabashin chana a gundumar Anhui.
Manyan jami’an diflomasiyya kuma wakilai daga kasashen akistan, Iran, Russia, Tajikistan, Turkmenistan, da kuma Uzbekistan ne dai ake sa ran zasu halarci taron.
Ministan harkokin wajen gwamnatin taliban Amir Khan Muttaqi ma zai halarci taron yayin da kasashen Indonosia da Qatar zasu halarta a matsayin baki, kuma kasa chana zata zama mai masaukin baki a yayin gudanar da taron.
Taron dai irin sa na farko dana biyu an gudanar a kasashen Pakistan da Jamhuriyar musulunci a shekarar data gabata.
Majiyoyin chana kuma sun tabbatar da cewa Lacrov zai halarci wani taro na daban da ak yima suna da “Extended Troika” wanda ya kunshi Chana, Afghanistan da kuma Amurka.
Chana, Pakistan, Rasha da kuma Amurka wasu kasashe da suke da tasiri a kan lamarin mutanen afghnistan a ta bakin kakakin fadar gwamnatin rasha Wang Wenbin a wani taron manema labarai daya gudanar a yau laraba.
Kasar Afghanistan dai ta shiga yanayin hargitsi tun bayan da taliban wacce a baya ta taba mulkar kasar daga 1996 to 2001 ta kuma karbe madafun iko kuma ta shelanta kafa gwamnatin rikon kwarya a ranar 15 watan augustan wannan shekarar.
Dawowar taliban yana zuwa ne biyo bayan ficewar gaggawa kuma ba shirin da Amurka tayi daga kasar ta Afghanistan.