Rabiu Musa Kwankwaso yace bai hakura da neman zama shugaban kasar Najeriya a 2023 ba Kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Muyi Fatosa Fatosa ya ce ‘Dan takaran na NNPP bai janye ba, kuma sam bai yi wa Bola Tinubu mubaya’a ba.
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanya cewa sun yi wa Asiwaju Bola Tinubu mubaya’a a zaben 2023.
A wata sanarwa ta musamman da ta fito daga kwamitin yakin zaben shugaban kasar, an tabbatar da cewa ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP bai janye ba. Sanarwar ta ce Rabiu Kwankwaso yana takarar zama shugaban kasa, kuma bai damu da rahotannin karyan da ke nuna yana goyon bayan Bola Tinubu ba.
“Kwankwanso yana cigaba da samun goyon baya daga mafi yawan mutanen Najeriya. Abin da Kwankwaso ya fada Domin karin-haske, sanarwar ta fadi abin da Kwankwaso ya fada a hirar da ya yi da Dr. Reuben Abati na gidan talabijin Arise TV a game da Bola Tinubu.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani karara cewa: “Bola Tinubu aboki na ne na tsawon shekaru, da ba na takara, na bada shawarar a zabe shi.”
Ba na yin siyasar gaba, dukkanninmu ‘yan takarar shugaban kasa ne, amma na fi cancanta.”
Muyi Fatosa Hadimin ‘dan takaran, Muyi Fatosa wanda ya fitar da wannan jawabi a Facebook, ya ce abin takaici ne a juya kalaman, ana cewa yana tare da Bola Tinubu.
A rika tantance labarai “Kwamitin yana mai matukar karyata wannan rahoto na cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bi Tinubu, tana kira ga mutane su rika tantance labarai.”
“Kwamitin yana karfafawa masu ruwa da tsaki, ‘yan jam’iyya da magoya baya su yi watsi da wannan karya, su cigaba da goyon bayan wanda ya dace.”
“Mu na kara tabbatarwa mutanen Najeriya da dinbin magoya bayan Rabiu Kwankwaso a gida da waje cewa shi ne ‘dan takaran da za gwabza da shi.”
Muyi Fatosa Dalung ya ziyarci Kwankwaso Mu na da rahoto an ga Barr Solomon Dalung wanda tsohon Minista ne a Najeriya a gidan Rabiu Musa Kwankwaso, ya je gaisuwar yawon sallah a Kano Har yanzu ba mu da masaniyar ko ‘dan siyasar na jihar Filato ya shiga jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi, duk da an gan shi dauke da jar hula.