Kasar Faransa ta kwashe sojojin ta daga tsakiyar birnin Burkina Faso kwanaki bayan zanga zangar kyamar zamansu a yankin da al’ummar kasar ke ci gaba da yi.
Mai magana da yawun sojin faransa din Kanar Pascal Ianni ya ce tawagar sojin da ke dauke da kayan aiki ta bar Kaya a ranar asabar domin isa Jamhuriyar Nijar.
Jami’in ya ce dalilin kwashe sojojin daga wurin shi ne kaucewa arangama sakamakon tankiyar da aka samu.
A wani labarin na daban ojojin Burkina Faso uku sun gamu da ajalinsu, wasu bakwai kuma suka jikkata, a wani kazamin hari da aka kai masu a daidai kan iyaka da kasar Ivory Coast.
Tun shekara ta 2015 ne dai kasar Burkina Faso ke fuskantar yawaitan hare-hare daga masu ikirarin jihadi da karfin tsiya da suka mamaye yankunan kasashen Mali, Nijar.
Majiyoyin samun labarai sun bayyana cewa babu wanda zai iya gane wadannan mahara, da suka kai harin a yankin Mangodara a daidai karfe 9 na daren littini.
Raunin da wasu suka samu yayin wannan hari babu kyau.
Sai dai kuma wasu majiyoyin na cewa sojan sun sami nasarar kasha masu jihadin 6.
Mako daya kenan aka sami irin wannan hari, inda aka jikkata wani dan-sanda, da kasha wani mahari a kauyen Tehini dake kan iyakan Burkina da Ivory Coast