A karon farko tun bayan rikicin Rasha da Ukraine, wani jirgin ruwa ya tunkari kasar Ukraine domin dibar tsaba zuwa nahiyar AFrika.
An bayyana jirgin ruwan zai nufi kasar Habasha a karkashin wani shiri da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya na fitar da hatsi daga Ukraine domin shawo kan matsalar abinci a duniya.
Rikicn Rasha da Ukraine manyan kasashe wajen samar da alkama ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo a duniya tare da haifar da matsalar karancin abinci a kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da kuma wasu sassan Asiya.
A cikin ‘yan kwanakin nan, jiragen ruwa da yawa masu jigilar hatsi sun bar tashoshin jiragen ruwa na Ukraine a karkashin sabuwar yarjejeniyar, amma yawancin jigilar kayayyaki abinci ne na dabbobi.
A ranar Juma’a, shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za a yi lodin kayan agaji na farko da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya zuwa Afirka, kuma hatsin da za’a kai kasar Habasha, na daga cikinsu.
Jirgin mai suna Brave Commander, ana sa ran zai dauki fiye da ton 23,000, a cewar ma’aikatar samar da ababen more rayuwa ta kasar Ukraine.
Habasha, tare da Somaliya da ke makwabtaka da Kenya, na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru arba’in a yankin kahon Afrika