Jarumar Fatima Mohammed na ɗaya daga cikin jaruman finafinan da ke fitowa a Masana’antar Finafinan Hausa ta Kannywood.
Jarumar mai shekaru 25 da aka fi sani da Sangaya, ɗaya ce daga cikin sababbin fuskoki da aka sani a masana’antar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
A wannan hirar, jarumar ta yi bayani kan shahararta da sauransu:
Mene ne tarihinki a taƙaice?
Sunana Fatima Mohammed wadda aka fi sani da Sangaya. An haife ni a Maiduguri Jihar Borno, kuma na girma a Abuja.
Jarumar ta bayyana cewa ta yi karatun firamare da sakandare a Abuja daga baya na koma Jihar Borno, inda na yi jarrabawar kammala sakandare (SSCE) kafin in shiga harkar fim na wasu shekaru.
Me ya jawo ra’ayinki kika fara wasan kwaikwayo?
A gaskiya zama ’yar fim ba burina ba ne. Ba kamar sauran masu fasaha ba, ban taɓa sha’awar zama ’yar wasan kwaikwayo ba, musamman bayan kammala karatuna na sakandare.
Shigata harkar fim ta samo asali ne ta dalilin wata ƙawata. Mun kasance aminan juna sosai.
Wannan ƙawar tawa tana son shiga harkar wasan kwaikwayo, amma iyayenta sun hana ta, har sai ta kammala karatunta na sakandare.
Ƙawancenmu da kusancinmu ya kasance duk abin da ya shafi ɗayarmu babu shakka yana damun ɗayar.
Mun yi nasarar shawo kan iyayenta su bar ta, ta shiga harkar wasan kwaikwayo. A haka ne shigata Kannywood ta fara.
Me iyayenki suka ce game da shawararki ta shiga Kannywood?
A bayyane take cewa akasarin iyaye suna damuwa a kan ’ya’yansu da ke yanke shawarar shiga masana’antar shirya finafinai.
Haka ni ma nawa iyayen abin yake. Sun nuna damuwarsu da farko, amma daga baya, sai suka haƙura, suka ba ni izini, tare da gindaya min sharuɗɗan da zan bi kuma in yi nasara.
Finafinai nawa kika fito a ciki?
Kodayake ban daɗe a masana’antar ba, amma na fito a cikin finafinai da yawa.
Na yi finafinai kamar, Mai Martaba da Alaƙa da Ruɗani da Matar So da Ke Duniya da Abokin Tafiya da sauransu. Na taka rawa a fim ɗin Mai Martaba kuma fim ɗin ne ya sanya min sunan Sangaya.
Wane amfani kika samu a masana’antar tun shigarki?
A gaskiya ban taɓa tunanin masana’antar za ta canza ni haka ba.
Idan na ce canzawa, ina nufin canza halin rayuwata gaba ɗaya. Ina faɗin haka ne bisa irin basirar da na samu a masana’antar.
A hankali, na samu damar kasancewa wani abu, kuma yanzu ina cuɗanya da mutane cikin sauƙi.
Na kasance mai zafin rai, amma kasancewa a masana’antar ta canza ni kwata-kwata zuwa wani hali na daban.
Waɗanda suka san ni yawanci suna bayyana mamakinsu game da yadda halayena suka canza.
Masana’antar ta koya mani yin haƙuri, juriya da ƙanƙan-da-kai. Har ila yau, masana’antar ta koya mini yin abin da nake so a matsayina ta ’yar wasan kwaikwayo kuma kada in yi watsi da abin da na san shi ne daidai.
Yaya za ki kwatanta ranarki ta farko?
Ƙwarewar tana nan tamkar sabuwa a kullum. Na fara a matsayina ta ɗaliba kuma na yi aiki tare da ƙawayena.
Kodayake shi ne wasan kwaikwayo na farko, na samu damar yin komai daidai, inda ta kai har mutane da yawa suna tunanin cewa na taɓa yin wasan kwaikwayo a baya.
Wannan rawa da na taka ta nuna ƙwarewa, ta sa na samu canjin tunani, kuma ta koya min yin mu’amala da mutane ba tare da la’akari da ɗabi’arsu ko halinsu ba.
Na ji daɗi sosai na yi mamaki, kuma ya zame min abin tunawa, musamman lokacin da fim ɗin ya fito. Kullum ina sha’awar son jin martanin mutane kan irin rawar da na taka.
Da yawa sun yi watsi da masana’antar saboda jifar su da munanan kalamai da ake dangantawa da rawar da suka taka, yayin da da yawa suka amince su ci gaba da zama a cikin masana’antar duk da irin maganganun da suke ji.
Mece ce shawararki ga jarumai mata?
A duk inda mutum ya tsinci kansa, akwai buƙatar ya kiyaye mutuncinsa, haka kuma mutum ya fahimci cewa, ko mene ne yana da rawar da zai taka wajen kare kyawawan ɗabi’u da al’adunmu da addininmu.
Ba wanda zai girmama ka idan ba ka girmama kanka ba. Ya kamata a koyaushe mu kasance da tunanin cewa ba mu muka kai kanmu wannan matsayi ba.
Mene ne burinki a matsayinki na jaruma?
Da yawa daga cikin jaruman finafinai a Kannywood, suna da burin zama furodusoshi, amma burina shi ne in zama fitacciyar mai tace finafinai wato Edita, tare da kasancewa mai fassara abin da ake faɗa a fim wato (sub-title).
Duba Nan: APC Ta Kori Ganduje Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Ina kuma so in ci gaba da karatuna.