A yayin da shekarar 2021 ke zuwa karshe, ya dace mu tuna da jerin wasu abubuwan da suka faru a cikin shekarar.
Masana’antar Kannywood ta fitar da jerin fina-finai daban-daban wadanda suka dauka hankalin masu kallo matuka.
Hakazalika, wasu fina-finan sun yi shuhura a wannan shekarar inda masu kallo suka dinga kwasar nishadi da jin dadi yayin kallonsu, lamarin da yasa suka yi matukar tashe a shekarar nan. 33.4K Jerin fina-finan Kannywood 5 da suka yi tashe a shekarar 2021.
Mun tattaro muku wasu jerin fina-finai 5 da suka yi matukar tashe a cikin shekarar 2021.
1. Labarina Babu shakka fim din Labarina ya yi matukar tashe a cikin shekarar nan. Abubuwa masu yawa sun ja hankalin masu kallo zuwa kallon fim din mai dogon zango.
2. Izzar so Wannan shiri ne mai dogon zango wanda jarumi Lawan Ahmad ya shirya shi kuma ake sakinsa a kowanne mako. Wannan shirin ya ja hankalin mutane saboda ya dauko sabbin ‘yan wasa wadanda suka matukar taka rawar gani wurin wasan kwaikwayon.
3. Fanan Babu shakka fim din Fanan ya dauka hankali jama’a masu tarin yawa. Tun kafin fitar fim din a sinima, an dinga tallarsa kuma wakar da ke ciki ta matukar kayatar da jama’a. Wannan fim din na tsohuwar jaruma Mansurah Isah ne inda tsohon mijinta tare da diyarta Iman Sani Danja suka bayyana.
4. Gidan Badamasi Wannan shirin mai dogon zango ya ja hankalin masu kallo duk da kuwa ba wannan shekarar aka fara yin sa ba. Dalilin kuwa da yasa hankalin jama’a ya karkata kan wannan fim din shi ne sabbin ‘yan wasa da aka kara a ciki.
5. Kwana Casa’in Shirin kwana casa’in shiri ne mai dogon zango mai cike da ‘yan wasa tsofaffi da kuma masu tasowa. Akalar shirin ta karkata ne kan yanayin tsarin shugabanci, siyasa da kuma yaki da rashawa.
Tabbas masu kallo suna daukin wannan fim da ake fitarwa a kowanne mako. Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021 A wani labari na daban, masana’antar Kannywood dai na kunshe ne da jarumai masu tarin yawa.
Akwai tsoffin jarumai, sabbi da kuma masu tasowa. Wasu sun yi suna ne a wannan shekarar sakamakon rawar da suke takawa a wasu fina-finai masu dogon zango.
A cikin shekarar nan ta 2021, akwai jaruman da tauraruwarsu ta fi haskawa sakamakon wata rawa da suka taka a wasu sabbin fina-finai ko kuma makamancin hakan.