Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, a ranar Laraba, ya ce gwanda yan Najeriya su daina yaudarar kansu cewa abubuwa na tafiya daidai a Najeriya.
Sultan Saad ya bayyana hakan ne a taron tattauna matsalar tsaro dake gudana a Abuja, rahoton Channels. “Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwa na tafiya daidai, abubuwa sun tabarbare.
Mun san hakan, kuma muna gani,” Sultan yace. “Abubuwa sun yi muni yanzu. Ba ka bukatar wani ya fada maka Najeriya na cikin halin ha’ula’i kuma wannan shine gaskiya.
” Sarkin ya yi bayanin cewa a shekaru 11 da yayi matsayin Sarkin gargajiya, ya halarci tarukan tattauna matsalar tsaro a Najeriya da dama, kuma lokaci ya yi da shugabannin zasu tashi tsaye maimakon surutai.
Sultan ya yabawa Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila, kan shirya wannan taro. Ya yi kira gareshi ya tabbatar da cewa an aiwatar da shawarin da aka samu bayan taron.
Sarkin ya bayyana farin cikinsa cewa Kakakin majalisar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad, sun amince abubuwa sun lalace a kasar nan.
Najeriya na fama da matsalolin tsaro ta kowace fuska. Daga Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, zuwa matsalar yan bindiga a yankin Arewa maso yamma, sai kuma rikicin manoma da makiyaya a Arewa maso yamma, yan ta’addan IPOB a kudu maso gabas da kuma garkuwa da mutane a Kudu maso yamma.
Masu hankali dai suna ganin gwanda hankalin mai saran kaba ya koma ga rina domin dai an tabbatar da cewa abubuwa sun lalace sosai da sosan gaske najeriya musamman arewacin najeriya, wanda ana ganion gwanda yanayin kdancin najeriya a kan arewacin najeriya din ma.
Kiran sarkin musulmin yazo a dai dai lokacin da ake matukar bukatar sa duba da mawuyacin halin da tsaron kasa musamman arewacin najeriyar ya fada ciki.
Al’ummar najeriya dai sun zura idanu domin ganin ta inda hannun ceto zai riske su.