Shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce babu banbanci tsakanin kungiyoyin masu aikata laifuffukan dake fakewa da sunan masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB da ta masu kokarin kafa kasar Yarbawa zalla a bangare guda da kuma boko haram da ISWAP a daya bangaren saboda yadda suke adawa da duk wanda ya saba da irin ra’ayoyin su.
Shugaban majalisar ya bayyana kungiyar batagarin dake fakewa da IPOB da ta Sunday Adeyemo dake nema kafa kasar Yarbawa zalla a matsayin masu barazana ga zaman lafiyar Najeriya, inda yake cewa ya dace a dauki mataki akan su.
Gbajabiamila yace yayin da aka karkata akalar sha’anin tsaron Najeriya wajen yaki da ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindigar da suka addabe ta, ya zama wajibi a kara damuwa dangane da bullowar wadannan batagarin dake fakewa da sunayen wadannan kungiyoyi suna yiwa kasa barazana.
Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaban majalisar na cewa bata gari da masu aikata laifuffuka na fakewa da sunan ‘yan aware suna haifarwa Najeriya matsaloli da kuma yi mata zagon kasa.
Gbajabiamila ya bayyana wadannan mutane a matsayin wadanda suka haifar da mummunar matsala ga sauran jama’ar kasa, ta hanyar illar da suke musu wajen kai musu hari da kuma lalata dukiyoyin su tare da kadarorin gwamnati da na al’umma saboda kin goyan bayan abinda suke so.
Shugaban majalisar yace idan akayi nazari akan wadannan matakai, toh babu tantama ayyukan wadannan kungiyioyi sun yi daidai na kungiyoyi irin su boko haram da ISWAP, kuma da zaran an basu dama zasu durkusar da Najeriya baki daya.