Rahotanni dake zuwa mana daga jamhuriyar musulunci ta Iran suna tabbatar da cewa shirye shirye sunyi nisa domin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Dakta sayyid ibrahim raesi.
Rantsuwar wacce ake sa ran za’a gudanar da ita babban birnin tehran zata samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen kasar wadanda suka hada da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar sayyid Ali Khamene’i.
Dakta Ibrahim Raesi wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar a kwanakin baya ana sa ran zai sha rantsuwar aiki a yau 3 ga watan augusta wanda yayi dai dai da 12 ga watan murdad a lissafin shekarar Iraniyawa.
Sabuwar gwamnatin dai ana sa ran tazo da sabbin hanyoyi domin warware matsalolin da ake ganin suna damun Iraniyawa ciki har da matsalolin tattalin arziki sakamakon takunkuman tattalin arziki da kasar amjurka ta kakaba ma kasar mai albarkatun man ffetur da sauran su.
Daga yau talata dai sabuwar gwamantin zata soma aiki inda zata fuskanci manaan batutuwa da ta gada daga tsohuwar gwamnati mai shudewa wanda suka hada ta tattaunawar neman matsaya tsakanin Iran din da sauran kasashen yammacin turai.
Iran dai na zaman kasar da tafi kowacce kasa fama da takunkuman tattalin arziki har ma dana kayan magunguna da lafiya wanda hakan ke zaman babbar matsala a kokarin jamhuriyar musulunci ta Iran din na samar da ci gaba mai dorewa a fadin kasar.
Jagoran juyi dai na Iran din sayyid Ali Khamene’i ya jima da bama sabuwar gwamnatin shawara da cewa ta dauki darasi daga kusa kuren gwamnati mai shudewa wanda daga ciki har da gujewa ta’allaka tattalin arzikin kasar ta Iran da romon bakan kasashen ketare.
Dangane da sabon shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran din an shaide shi da gaskiya da rikon amana gami da rashin wasa a lamuran aiki tun daga lokacin da ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikacin kotu har zaman sa shugaban haramin Imam Ridha (S.a), har ya zama alkalin alkalan kasar wanda daga nan ya lashe zaben kujerar shugabancin kasar a kasa da watanni biyu da suka gabata.