Rahotanni faga babban birnin tarayya Abuja suna nuna ranar lahadi shugaba muhammadu buhari zai bar najeriya, inda zai tafi domin halartar taron majalisar dinkin duniya ranar 19 ga satumba, taron da za’a fara shi ranar 14 ga satumbar wannan shekara ta 2021.
Taron wanda za’a kammala shi ranar 27 ga satumba, rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda zasuyi tafiyar tare da buhari zasu tafi tun ranar talata inda buharin zai tarar dasu a amurkan ranar lahadi domin halartar wannan taron na majalisar dinkin duniya.
Rahotanni daga majiya mai tushe sun tabbatar da cewa gwamnatin shugaba buhari ta fara tura shugaban ma’aikata, Gambari wanda jami’in diflomasiyya ne kuma tsohon dana majalisan dinkin duniya ne, tare da sauran abokan aiki sa ne domin tabbatar da cewa sun kashe duk wata kura da zata iya tasowa daga ‘yan najeriya mazauna amurkan kafin buharin ya isa amurkan.
Dama dai a kwanakin baya Gambarin ya ziyarci amurkan inda ya bi hanyoyin daya tabbatar ya lalata wani yunkurin na mazauna najeriyar dake amurka wanda wanda suka shirya domin nuna rashin amincewar su d salon mulkin shugaba buhari.
Shugaban dai yana shirin wannan tafiyar zuwa amurka ne a dai dai lokacin da ake cikin matsanancin halin rashin tsaro gami da tsadar rayuwa a najeriyar wanda hakan yake zaman babbar barazana ga rayukan miliyoyyin al’ummar najeriya.
Rahotanni dai daga amurkan sun tabbatar da cewa a 11 ga watan agustan wannan shekarar da muke ciki ne wasu gamayyar kungiyoyi na ‘yan asalin najeriya mazauna amurkan suka shirya zasu gudanar da wani gagarumin gangami wanda zai kunshi miliyoyin mutane domin nuna rashin amincewar su da salon mulkin buhari kuma suyi kira da ayi rafarandom a najeriya domin fayyace makomar najeriya amma rahotanni daga majiya mai tushe sun tabbatar da cewa sai da gwamnatin ta buhari ta shiga ta fita ta tabbatar wanna gangami bai yiwu ba.