Rahotanni daga Najeriya na cewa rufe kasuwanni a wasu jihohin arewa maso yammacin kasar na yin mummunan tasiri a kan ‘yan bindiga da suka saba cin karensu ba babbaka a yankunan, inda har suka fara karbar abinci dangin su shinkafa da taliya a matsayin abin fansa a kan wadanda suka sace.
Wani mazaunin Sabon Birni da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana yadda aka saki ‘yan makwafcinsa bayan da aka bada mudu 10 na shinkafa.
Wadanda ke bibiyar al’amarin sun ce matsalar ‘yan bindiga din ta ta’azzara ne bayan da aka dakile layukan sadarwa, inda a halin da ake ciki ‘yan bindigar sun shiga wani hali na rudani.
A wani labarin na daban mafarautar gargaji a Najeriya sun yi nasarar kashe ‘Yan bindiga 47 da suka hana mutanen Shiroro dake Jihar Niger zaman lafiya na dogon lokaci.
Majiyar jaridar tace ‘Yan bindigar sun dade suna amfani da ‘yankin dake kusa da gabar ruwa wajen fakewa suna kaiwa jama’a hare hare a yankunan jihar.
Jaridar tace wani jami’in ‘Yan sanda ya tabbatar mata cewar bayan kashe 47 daga cikin su, wasu da dama sun tsere da harbin bindiga a jikin su.
Jihar Niger na daya daga cikin jihohin da ‘Yan bindiga suka hana jama’a sakewa, inda suke kai hari garuruwa suna kashe mutane da kuma kwashe wasu domin karbar kudin fansa.
Bello yace ‘Yan bindigar sun jefa jama’ar sa cikin halin kakanikayi wajen hana ‘yayan su zuwa makaranta da hana jama’a tafiye tafiye da gudanar da harkokin noma, amma kuma ba zasu bada kai bori ya hau ba.