Ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka, ya ce rahoton hukumomin leken asirrin Amurka game da binciken asalin kwayar cutar COVID-19, bai gabatar da amsar da Amurkar ke bukata ba.
Yana mai cewa, ci gaba da yunkurin ba abun da zai haifar, saboda ya saba da kimiyya kuma dama abu ne da babu shi.
A jiya Jumma’a, ofishin daraktan hukumar leken asiri ta Amurka, ya gabatar da takaitaccen bayani kan nazarin asalin cutar COVID-19, wanda kuma bai soke yuwuwar fitowar kwayar cutar daga halitta ko dakin gwaji ba.
Sanarwar da ofishin jakadancin Sin ya fitar, ta ce kasar Sin na adawa da babbar murya da kuma tir da rahoton, har ma da sanarwar da fadar White House ta fitar a jiyan, wadda ke cewa, kasar Sin ta yi kokarin kawo tarnaki ga binciken kuma ta yi watsi da kiran da aka yi na tabbatar da gaskiya, tana mai kira ga kawayenta da su matsawa kasar Sin lamba. (Fa’iza Mustapha)
Kasar amurka dai na kokarin mayar da lamarin annobar cutar covid19 siyasa, inda take da burin kakabawa kasar Sin alhakin samuwar annobar cutar korona wanda hakan zai bada damar kakabawa kasar ta Sin takunkuma wadanda zasu iya karya tattalin arzikin kasar.
Kasar Sin dai na cikin kasashen da suka zamewa amurka barazana musamman a bangaren tattalin arziki da karfin soji.