Yayin da gobe Lahadi in Allah Ya kai mu za a yi Babbar Sallah a bana, rahotannin da wakilanmu suka tattaro mana sun nuna cewa bikin Sallar na bana zai gudana ne a cikin kogin talauci a daidai kuma lokacin da ake fama da tsadar rayuwa da kunci.
A Abuja, Aminiya ta gano cewa magidanta da dama da suka saba sayan raguna don yankawa a Sallar Layya suna cikin halin zulumi sakamakon gaza yin hakan saboda tsadar rayuwa da al’ummar kasar nan ke fuskanta.
Yawancin wadanda Aminiya ta zanta da su a yankin Birnin Tarayya Abuja, sun yi korafin cewa tsadar kayan abinci ba za ta ba su sukunin sayen dabbar Layya ba, wadda ita ma farashinta ya karu da ninki biyu zuwa uku.
Wani matsakaicin ma’aikaci a Abuja mai suna Sani Ahmad, ya ce zuwa ranar Talatar da ta gabata saura kwana 5 a yi Sallar ba ya da abin da zai sayi dabbar Layya sakamakon yadda abincin yau da kullum ke cinye da kudin albashinsa.
Ya ce akwai ma’akata da dama da ke sama da shi da suke da korafi irin nasa.
Abubakar Ibrahim, wani dan kasuwa a Abuja ya ce zai yi wuya ya iya sayen dabbar Layya a bana saboda farashinsu da ya daga sosai, ga kuma nauyin kasuwa da yake fama da shi.
Ya ce ya gwammace karkata da kudi ta bangaren noma da yake yi a bana sakamakon tsadar kayan abinci.
Aminiya ta ziyarci Babbar Kasuwar Dabbobi ta Abuja da ke Dei-Dei inda yawancin masu sayar da dabbobi a kasuwar, suka yi korafin rashin ciniki.
Sun ce lamarin na zuwa ne a lokacin da adadin dabbobi da aka saba kaiwa kasuwar ya ja baya saboda raguwarsu a wasu jihohin Arewa da ke gaba-gaba a wajen kiwonsu kamar Zamfara da Katsina da Sakkwato da matsalar tsaro ta haifar.
Alhaji Uzairu Dan-Kundalo daga Jihar Jigawa ya ce haka kuma wasu masu kiwon dabbobi ko sayar da su da ke kawo ragunansu zuwa Abuja a lokacin Sallar, da alama a bana sun gwammace sayar da dabbobin a jihohinsu saboda tsadar kudin mota da shigowar damina, da suke jin ba za su bar gonakinsu ba.
Ya ce a baya ma’aikatu da kamfanoni da ke Birnin Tarayya kan sayi dabbobi da yawa daga hannunsu don rarraba su ga ma’aikatansu.
“Sai dai a yanzu wadanda ke saya daga wannan bangaren kadan ne kawai, haka ma dadaikun mutane da ke sayen biyu zuwa 10 don raba su ga makusantansu sun ja baya a dalilin tsadar rayuwa,” inji Dan-Kundalo.
Binciken Aminiya ya gano cewa, Kasuwar Dabbobi ta Dei-Dei ta rabu biyu inda ake da bangaren ’yan kasuwan dindindin da ke sayar da dabbobinsu a cikin rumfuna da kuma tsakiyar kasuwa.
Akwai kuma bangaren baki da suke zuwa a lokacin hadahadar Sallah kadai, da aka ware masu wuri a gefen kasuwar, da ba ko wane mai shigowa ba ne zai iya gano su.
Alhaji Haruna Ahmad da ya kai raguna kasuwar daga garin Gangalawai a Karamar Hukumar Darazo a Jihar Bauchi, ya ce tsadar abincin dabbobi da ya ninka daga bara zuwa bana, na cikin abubuwan da suka kara tsadar dabbobi a bana.
Ya yi misali da dusa da a bara ya ce sun saye ta a kan Naira dubu 12 zuwa dubu 13. Ya ce sai ga ta ta kai Naira dubu 23 zuwa dubu 24 a bana.
Dan kasuwar ya ce haka lamarin yake a farashin kowar wake da suka saya Naira 6,000 a bara, amma a bana ta kai Naira 12,000 a yayin da farashin kaikayin dawa da a bara aka sayar kan Naira 3,000 a bara, a bana ya kai Naira 7,000.
Ya ce a bangarensu na baki da ake dauka a matsayin masu rangwame, ana iya samun karamin rago da ya kai yin Layya a kan Naira dubu 100, sabanin Naira dubu 60 da aka sayar a bara.
Ya ce matsakaicin rago na kaiwa Naira dubu 250 zuwa dubu 300, sabanin bara da ake iya samu a kan Naira dubu 150.
Dan kasuwar ya ce babban rago da aka turke na kamar shekara 3, na kaiwa Naira dubu 700 zuwa dubu 800.
Ya ce akwai koma-baya wajen ciniki a bana idan aka kwatanta da bara a kwatankwacin ranar zantawar, wato kwana biyar kafin Sallah.
Sai dai ya ce suna fatar samun ciniki a lokacin da zai rage kamar kwana uku kafin Sallah har zuwa ranar Sallah, lokacin da ya ce yawancin ma’aikata suka fi sayen dabba saboda karancin wuraren ajiye su a gida.