Kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Yusuf Bin Ahmad ya bayyana cewa tabbatar da tsaron kasar Iraki wajibi ne na kasashen musulmi baki daya.
Bin Ahmad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi kafin kammala zaman taron birnin Bagadaza a jiya Asabar.
Mahalarta taron na birnin Bagadaza sun bayyana matsalolin da yankin gabas ta tsakiya ke fuskanta a matsayin babban abu mafi muhimmanci da ya kamata su mayar da hankali a kansu domin samo hanyoyin warware su.
Taron na birnin Bagadaza wanda ya gudana a jiya, ya samu halartar shugaban kasar Faransa Emmanuel macron, da kuma sarkin Jordan, gami da shugaban kasar Masar, da kuma sarki Qatar, da Firayi ministan UAE, gami da ministocin harkokin wajen na kasashen Iran, Saudiyya, Turkiya, Kuwait, da kuma babban sakataren kungiyar kasashen larabawa, da kuma babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC.
A yayin taron bangarori daban-daban sun samu damar tataunawa da hakan ya hada shugabannin masar da Qatar wadanda a baya ba sa ga maciji da juna, kamar yadda kuma ministan harkokin wajen Iran Amirka Abdollahian ya gudanar da tattaunawa da bangarori daban-daban da suka wakilci kasashensu a taron.
Bayanin bayan taron dai ya jaddada wajabcin yin aiki tare a tsakanin dukkanin kasashe makwabtan Iraki da sauran kasashen yankin baki daya, domin samun mafita ga matsaloli da dama da suka addabi yankin baki daya.
Kasar Iraki dai na fama matsalolin tsaro sakamakon sojojin amurka da suka mamaye kasar tun shekarun da suka gabata amma ana sa ran wannan taron ya kawo daidaituwar lamurra da kuma kawo karshen tashe tashen hankula a kasar ta Iraki musamman yadda manyan kasashen musulmi na larabawa suka maida hankali kan tabbatar da cewa sojojin amurkan sun fice daga kasar ta Iraki mai arzikin man fetur.