Tuni dai Rafael Grossi, Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya isa birnin Tehran na kasar ta Iran don tattaunawa da takwaransa na kasar, Mohammad Eslami ranar Lahadi.
Tun bayan kama mulkin Shugaba Ebrahim Raisi wanda ya nada Eslami shugabancin hukumar a watan Agustan da ya gabata.
Duka bangarorin biyu dai sun bayyana tattaunawar a matsayin wacce ta yi nasara kuma sun amince su ci gaba da tattaunawar a gefen babban taron hukumar da zai gudana a birnin Vienna na Austria a cikin watan Satumbar nan.
Kazalika, sun kuma amince cewa Mista Grossi zai je Tehran nan ba da jimawa ba domin aikin sake na’urorin daukar hoto da na nadar bayanai da ke tashar inganta makamashin Nukiliyar ta Iran, kamar yadda yake a wata sabuwar dokar da Majalisar Dokokin kasar ta amince da ita a watan Disambar bara.
Tun a watan Fabrairu ne dai Iran ta amince cewa za ta mika na’urorin nadar bayanan ga hukumar bayan wata yarjejeniya da ta cimma a birnin Vienna wacce za ta kai ga dage takunkumin karya tattalin arzikin da Amurka ta kakaba mata.
Tattaunawar dai na zuwa ne kwana biyu bayan wasu sabbin rahotannin sirri na hukumar ta IAEA da suka bulla ta kafafen yada labarai da ke nuna shakkunta kan shirin na Iran.
Sai dai kasar ta tsaya kai da fata shirinta na inganta ma’adinin Uranium na zaman lafiya ne ba na kera makaman Nulkiliya ba.
Sai dai a ziyarar shugaban hukumar IAEA ta bayyana cewa ikirarin da Iran din tayi gaskiya ne kuma ana sa ran a samu mafita daga takukuman tattalin arzikin da amurka ta kakaba ma Iran din wanda ta kai har kayan ayyukan lafiya aka daina sayarwa da Iran din.
Ana ganin dai duba da yanayin raguwar tasirin amurka wannan karon ana iya samun daidaituwar lamurra domin dama amurkan ce take kawo matsala a tattaunawar Iran da kasashen turai.