A ziyarar ban kwana da ofishi wanda shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran dakta hassan rohani bisa rakiyar ministoci da manyan kusoshin gwamnatin sa suka kai masa a gidan sa dake babban birnin Tehran, jagoran addini kuma babban kwamandan jamhuriyar musulunci ta Iran sayyid Ali Khamene’i ya tabbatar da cewa amurka da kawayen a na kasashen yamma ba ababen dogaro bane domin magance samar da cigaban tattalin arziki da ingantuwar rayuwa.
Jagoran ya bayyana kasashen amurka dana yammacin turai a matsayin wadanda suka jima suna yaudarar jamhuriyar musulunci ta Iran, yayin jamhuriyar musuluncin ta shiga alkawurra dasu amma kowane lokaci jamhuriyar musulunci ta Iran tana cika alkawuran data amma kasashen yammacin turai bisa jagorancin amurka basa cika alkawuran su.
Jagoran ya tabbatar da cewa a kwai darasi mai girma a gwamnatin dakta rohana wanda sabuwar gwamnati zata dauka wanda daga ciki suka hada da rashin mika aminci ga turawan yamma da kuma gujewa dogaro da alkawuran romon bakan kasashen yammacin turan, wadanda basu da maraba da yaudara gami makirci.
Jagoran ya yaba ma gwamnatin ta rohani, inda ya bayyana cewa a bangarorin da gwamnatin ta rohani bata mika amincin ta ga kasashen yammacin turai ba taci nasarori amma a duk bangarorin da ta dogara da kasashen yammacin turai akasin nasara ta samu wanda wannan babban darasi ne ga sabuwar gwamnati wacce zata kasa aiki nan da sati daya mai zuwa.
Iran dai tana cikin manyan kasashen duniya wadanda karan su ya kai tsaiko kuma suka isa su fada aji, sa’annan suke da damar tankiya da amurka.
Ziyarar wacce ta bankwana ce wacce gwamnati mai shudewa ta kaiwa jagoran dama bisa al’ada kamar yadda aka saba duk gwamnatin da ta gama aiki ta kai kaima jagoran ziyara inda zai musu barka gami da bangajiya sa’annan ya ayyana bangarorin da ta samu nasara gami da bangarorin da ta samu matsala domin daukan darasi ga sabuwar gwamnati mai kama aiki.
Kusan watanni biyu da suka gabata ne dai aka gabatar da zabe a jamhuriyar musulunci ta Iran din inda Dakta Ibrahim Ra’esi ya lashe zaben da kaso mafi rinjaye kuma ake sa ran zuwa alhamis ta sama zai kama aiki.