Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya nada kwararren dan jaridar nan dan asalin Jihar Kano, Abdulaziz Abdul-aziz, a matsayin mai magana da yawunsa.
Abdulaziz, dai yana cikin fitattun ‘yn jarida da suka kware wajen binciken kwakwaf da bankado badakala a Nijeriya.
Lokacin da ya yi aiki da jaridar ‘Premium Times’, Abdul-aziz, ya bankado cogen takardar kammala NYSC ta Kemi Adeyosun, abin da ya yi sanadin ajiye mukaminta na Ministar Kudi.
Daga bisani ya yi aiki a matsayin mataimakin Edita jaridar Daily Trust na tsawon shekara biyu, wanda a nan ma ya bankado sirrin manyan ‘yan bindiga da suka addabi wasu jihohin Arewacin Nijeriya; irin su Bello Turji da Auwalu Daudawa.
Abdulaziz ne ya yi rahoton nan na musamman da yamutsa hazo kan ayyukan yan ta’addan daji, inda ya zanta da ‘yan bindiga.
A wata sanarwa da ofishin yada labaran dan takarar shugaban kasar, ya fitar wadda take dauke da sa hannun Tunde Rahman, ta ce Abdulaziz zai taimaka wajen kawo sauye-sauye a harkokin yada labaran dan takarar shugaban kasar.
A wani labari na daban, wasu ‘yan ta’adda da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari har cikin wata majami’a da ke Jan Tsauni a yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
An gano yadda suka jigata babban faston cocin inda suka bar shi a wahale tare da yin awon gaba da masu bauta har su ashirin da biyar.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 15 ga watan Janairun 2023 wurin karfe 10 na safe yayin da masu bauta suka tsunduma cikin ibada. Tuni dai jami’an tsaro suka bazama ceto wadanda aka sacen.
Source: LeadershipHausa