‘Yan bindiga sun sace wani jami’in kwastam a kan hanyarsa ta zuwa aiki a jihar Kuros Riba.
An ruwaito cewa, ‘yan bindigan sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kudin fansa kafin su sako jami’in.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce ‘yan bindigan sun zo a kwale-kwale ne.
An rawaito cewa an sace wani Sufeto Janar na Kwastam, Mba Ukweni Edu da yammacin ranar Juma’a da Ferry Point a yankin Eton Central na Biakpan dake Jihar Kuros Riba.
Jaridar Sunday Tribune ta tattaro cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1.00 na rana zuwa 2.00 na yamma, lokacin da wanda aka sacen da aka tura kwanan nan zuwa yankin Ikom, ya dawo Calabar daga sansaninsa.
Ukweni, wanda aka ce dan kawu ne ga masanin dokoki, Mba Ukweni, Babban Lauyan Najeriya (SAN), zai yi ritaya nan ba da jimawa ba, saboda an yi imanin cewa sabon mukamin nasa na shirye-shiryen ritayar ne.
Wata majiya, wacce ta ga yadda aka sace jami’in amma ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa manema labarai cewa: “Ya yi aiki a Jihar Kuros Riba da Calabar a da, amma a wannan karon an tura shi Ikom, ya zo ne dag Lagos.
Shi ma’aikacin Kwastam ne, har yanzu yana aiki kuma ba da dadewa ba zai yi ritaya.
Ya kamata ya kai shekaru kamar 50 ”. Ko da yake Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan sandan Jihar Kuros Riba, Igri Ewa, lokacin da aka tuntube shi, ya ce ba shi da masaniya.
“Ba ni da masaniya a yanzu, ba su sanar da mu ba”, sai dai dan uwan wanda aka sace, duk da haka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Wanda aka sacen kawuna ne; an sace shi ne a kan hanyarsa ta dawowa daga Calabar, a cikin Kuros Riba (Ferry Point). ”
‘Yan bindigan sun zo da bindigogi suna harbi don tsoratar da mutane daga bakin kogin. Wadanda ake zargi da satar ba su gaza biyar ba kuma sun zo ne a cikin kwale-kwale.
Lauyan ya kara da cewa, “masu garkuwan sun tuntubi dangin a ranar Asabar inda suka bukaci a ba su N100m, kuma an sanar da ‘yan sanda”
“Wannan shi ne karo na farko da muka taba samun irin wannan lamarin, muna tsammanin sun shigo ne daga Calabar saboda sun koma ta hanyar Akwa Ibom wanda ke nufin sun zo ne daga Calabar”, in ji SAN.
A wani labarin, Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo sun kame wasu mambobi shida na kungiyar tsagerun Biafra ta IPOB kan mutuwar wani jami’in dan sanda, Daily Trust ta ruwaito.
Ana zargin wadanda aka kamen da kashe Sgt Joseph Nwaka tare da yin awon gaba da makaminsa.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Orlando Ikeokwu ya fitar, ya ce an kwato bindiga kirar AK47 guda daya, bindigogi kiran gida guda hudu da kuma tabar wiwi da yawa daga hannunsu.