A safiyar yau litinin ne wanda yayi dai dai da 4 ga watan june jagoran juyin juya halin halin musulunci Sayyid Ali Khamne’i ya bayyana a taron dubunnan mutane da suka taru a hubbaren gwarzon da ya assasa nizamin Jamhuriyar Musuluncin Iran Ayatullah Sayyid Ruhullah Musawi Khumaini (Q.S) dake babban birnin tehran.
Ana lissafin dai wannan shine karo na talatin da biyar da ake gudanar da wannan taro na tunawa da wafatin Imam Khumaini, taron da kan samu halartar mutane daga sassa daban daban na duniya duk shekara.
Taron wanda ake gabatar dashi a babban birnin tehran duk shekara wannan karon yazo da wani sabon salo mai ban sha’awa bayan shafe shekara biyu ba’a gabatar dashi cikin jama’a ba saboda yanayin annobar cutar korona da aka shiga.
Wannan karon dai an gabatar da taron a bainar jama’a maimakon gabatarwa ta hanyar yanar gizo gizo da kuma kafafen yada labarai irin su gidajen talbijin da sauran su.
Iran dai tayi nasarar fatattakar cutar korona kuma anyi kwanaki ba’a samu wanda ya kamu da cutar ba ko guda daya wannan ba bada dama wannan karon karon aka shirya taron a bainar jama’a a hubbaren Imam Khumaini dake baban birnin na tehran.
A cikin jawabin da jagora sayyid Ali khamene’i ya gabatar ya bayyana Imam Khumaini a matsayin gwarzon da babu inda za’a ambaci ingilabin jamhuriyar musulunci ta Iran ba tare da sunan sa ba.
Jagora ya bayyana juyin juya halin jamhuriyar musulunci na Iran a matsayin juyi mafi girma da tasiri a tarihin juyin juye halin da aka taba yi a duniya kamar na faransa da na shurabi.
Daya juyo bangaren masu kokarin aikata wasu ayyuka domin cutar da nizamin jamhuriyar musulunci a Iran ya bayyana sunyi kuskuren lissafi domin nizamin jamhuriyar musulunci na Iran bai taba samun karfi da goyon bayan iraniyawa irin na wannan lokacin ba.