Sojoji da ‘Yan Sanda suna shirin dura a kan dakarun tawayen kungiyar IPOB, soma aika Jami’an ‘yan sanda zuwa kowace jiha da ke Kudancin Najeriya.
Shugaban kasa ya bada umarnin a ga bayan duk mai neman tada zaune-tsaye Ganin yadda ake fama da matsalar ‘yan tawaye a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, jami’an tsaro suna shirin tada dakarun da za su fuskanci matsalar.
Jaridar The Cable ta fahimci cewa sojoji da ‘yan sanda za su kaddamar da wani shiri na musamman domin a samu zaman lafiya a Kudu maso gabas.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin suyi abin da zai kawo karshen ta’adin da wasu miyagu suke yi.
“Yan IPOB sun dauko hayar sojoji fiye da 50, 000, sun sa a rundunar ESN, sun tara makamai da suka samu a hannun ‘yan sanda lokacin zanga-zangar #EndSARS.”
Wani jami’in tsaro ya cigaba da fallasa kungiyar, ya ce: “Suna ta shigo da makamai ta Kamaru, tare da hadin-kan ‘yan tawayen Ambazonia da ke Kudancin Kamaru.”
“Duk mako, IPOB na tura akalla maza da mata 2000 zuwa Kamaru domin a koya masu amfani da makamai”
A dalilin haka ne rundunar ‘yan sanda ta fara shiri a Kudu maso gabas domin kai wa ‘yan tawayen hari.
An fara baza jami’an ka-da-ta-kwana zuwa jihohin yankin.
An kai mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda uku da runduna ta musamman zuwa kowace jiha. Su ma rundunar sojoji suna shiri na musamman ta yadda za su hada-kai da ‘yan sanda, domin su lallasa duk inda sojojin ‘ya ta’addan suke da nufin a kawo karshensu.
Gwamnatin Najeriya ta na sa ran shigowar wasu kayan fada kwanan nan, daga ciki har da jiragen yaki da za a kawo daga kasar Amurka da sojoji za su yi aiki da su.
A yau kun ji yadda mutanen Kungiyar IPOB suka yi sanadiyyar da wasu suka rasa motocin man-ja da suka dauko kaya daga garin Nsukka, za a kawo jihar Kano.
Shugaban kungiyar Galadima Road Transport ya bayyana cewa su na zargin ‘Yan ta’addan IPOB ne suke kai hari, suka barnatar dukiyar da su ka dauko daga Kudu.