Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, Human Rights Watch, ta ce sojoji Najeriya ba su da wata hujjar kashe ‘yan Shi’a a Zaria, duk da ikirarin da suka yi cewa mabiya Shi’ar sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai.
A wani rahoto da kungiyar ta fitar ta ce shaidun da ta tattauna da su sun gaya mata cewa sojoji sun kashe ‘yan Shia fiye da 300 a kwanakin biyu da suka kwashe suna yi musu luguden wuta.
Human Rights Watch ta ce , “Mun tattauna da shaidu 16 da kuma wasu biyar — cikinsu har da shugabanni — wadanda suka gaya mana cewa sojojin Najeriya sun yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi a cibiyoyi uku na ‘yan Shi’a a Zaria daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Disamba. Ba zai yiwu a ce tare hanyar da ‘yan kungiyar suka yi ya zama hujjar kashe daruruwan mutane ba”.
Kungiyar ta kara da cewa, “Sojoji sun kai hare-hare kan cibiyar Hussainniya Baqiyyatullah, da gidan shugaban ‘yan Shi’a, Sheikh Ibrahim Al Zakzaky da gidajen makwabtansa da ke Gyellesu da kuma makabartar ‘yan Shi’a, Daral-Rahma, a cikin kwanaki biyu. Shaidu sun gaya mana cewa sojojin sun kashe akalla ‘yan Shi’a 300 ko fiye da haka”.
‘Musanta adadi’
Haka kuma kungiyar ta ce sojojin sun binne mutanen da suka kashe a manyan kaburbura ba tare da amincewar ‘yan uwa da danginsu ba.
Human Rights Watch ta ce dole ne kwamitin da gwamnati ta kafa domin gano musabbabin rikicin ya yi aiki ba tare da nuna son kai ba, tana mai cewa dole ne a hukunta duk mutumin da aka samu da laifi.
Rundunar sojin Najeriya dai ba ta yi raddi kan wannan rahoton ba, sai dai a baya ta sha nanata cewa ta dauki mataki kan ‘yan Shi’ar ne saboda sun yi yunkurin hallaka Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai.
Kazalika, rundunar sojin ta sha musanta cewa ta kashe ‘yan Shi’a da dama a arangamar da ta yi da su.