Kotun Shari’ar Musulunci mai zama a Kofar Nasarawa karkashin alkali Sarki Yola, ta zabi yau a matsayin ranar yanke hukunci kan shari’ar Sheikh Abduljabbar.
Tun a watan Yuli na shekarar 2021, gwamnatin Kano ta gurfanar da Malamin a Kotu kan zargin maganganun ɓatanci ga Annabi SAW.
Wannan itace zama ta 30 da za’a yi tun bayan sama da shekara guda ana yi.
1:40 Yamma Kotu Ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa A cewar Alkali: Sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka: Anyekewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya.
Sashi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda.
Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu.
Kotu ta umarci hani da saka karatunsa Gidajen radio Gidajen Tv Da kafafen sadarwa Kotu ta bashi damar daukaka kara nan da kwana 30 12:41 Yamma Lokacin hutu ya kare, Alkali ya fara rubuta hukunci.
Bayan hutun kimanin mintuna ashirin da aka yi, an dawo daga hutun.
Wakilin Legit ta aiko mana da rahoton cewa: “Shi kuma alkali ya shiga wani ofishi sannan ya fara rubuta hukunci.
Kuma ya nuna baya neman ko wanne irin sassauci daga wajen Alkali.”
12:23 Yamma An tafi hutun rabin lokaci, sai 12:45pm za’a dawo.
Bayan dakatar da Abduljabbar daga magana, an tafi hutun rabin lokaci. An dage zaman sai zuwa karfe 12:45pm.
Wakilin Legit dake kotun yace: “Yanzu an daga shari’ar sai daya saura kwata za’a kotu…
Shari’a ce da za’a iya cewa tazo karshe tun da an riga an tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa shi wanda gwamnati ta shiga kara kan zargi da kuma abubuwan da ake masa”
12:20 Yamma Kafin yanke hukunci, AbdulJabbar ya ce Alkali karya yake masa Abduljabar ya fara fadawa Alkali kotun maganganun kare kan sa kuma ya nuna da Allah ya dogara.
An dakatar da Abduljabar daga maganganu. 12:14 Yamma Alkali ya tabbatar da laifi kan AbdulJabbar.
Mai shari’a Sarki Yola yace ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma’aiki.
Mai shari’a ya tabbatar da cewa maganganun fassara haxisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma’aiki.
Mai Shari’a ya fara karanta takardun kara, kafin yanke hukunci.