Babbar kotun dake Umuahia a jihar Abia ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta biya Nnamdi Kanu diyyar Naira Biliyan daya saboda cin zarafin da aka masa.
Kanu ya shigar da karanne gaban kotu inda yake neman a kwatar masa hakkinsa daga hannun gwamnati saboda cin zarafi.
Kanu ya nemi a biyashi biliyan 5 amma Mai shari’a Benson Anya yace a biyashi biliyan 1 sannan kuma gwamnatin tarayya ta bashi hakuri.
A zaman shari’ar da ake yi akanshi a Abuja kuwa, Kanu yace bai aikata laifin cin amanar kasa da ake zarginshi da yi ba.
Ya nemi a bada belinsa amma amma kotun ta ki amincewa.