Kasar morocco ta haramta fim din batanci na ”The lady of heaven” shirin fim din daya maida hankali wajen batanci da addinin islama.
Fim din the lady of heaven wani fim ne da aka shirya a kasar Ingila kuma hadin gwuiwa ne tsakanin wani kasurgumin bayahude Eli King da kuma wannan sanannen fitinannen da tawayen nan wanda ya shahara a kokarin haddasa husuma tsakanin bangarorin shi’a da sunnah a addinin musulunci watau yasir habib.
Hukumar kula da tace fina finai ta kasar morocco dai ta bi sahun sauran kasashen musulmi wajen haramta wannan fim, hakan kuma ya hada da shigo da fim din kallon sa da kuma duk wani lamari daya shafi wannan shirin fim wanda ake zargin yahudawa suka shiryo shi tare da hadin gwuiwar wasu daga cikin bara gurbin musulmai.
Ranar 3 ga watan yuni ake sa ran kaddamar da wannan lalataccen shiri amma tun kafin aje ko’ina manyan kasashen musulmi da dama sun haramta wannan shiri kamar yadda morocco ta haramta daga cikin kasashen da suka haramta a gaba gaba a kwai jamhuriyar musulunci ta Iran, sa’annan iraki, fakistan da dai suran su.
Wakilin mu ya tabbatar mana da cewa sakamakon bincike ya tabbatar da cewa musulmi a fadin duniya sunyi Allah wadarai da wannan shiri, kuma sun bukaci a gaggauta tsayar da masu shirya wannan shiri domin cin mutunci ne ga musulunci ta hanyar taba darajar diyar annabin rahama s.a.w.w.
Ba wadannan kasashe bama sauran kasashe da dama na duniya sunyi Allah wadarai da wannan shiri wanda ya maida hankali wajen batanci ga musulunci da musulmai.
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran sayyid Ali Khamene’i yayi ma shirin tofin ala tsine kuma ya bukaci al’ummar duniya musamman musulmi dasu kauracewa shirin fim din na batanci.
Ko jagoran gwagwarmaya na najeriya sheikh Ibrahim Zakzaky ma ya tona asirin mugun kullin dake karkashin wannan shiri a daya daga cikin jawaban sa.