A ranar Alhamis ne ake sa ran wata babbar kotu a jihar Kano a arewacin Najeriya za ta yanke hukunci bisa kisan da aka yi wa wata karamar yarinya Hanifa Abubakar.
Kotu na zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Dasambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.
Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.
Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A-Daidaita-Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi da ita.
A wani labarin na daban rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron kasar 12 a wani farmaki kan sansanin Sojin kasar da ke jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin kasar.
Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun koma kona wasu gine-ginen Sojin baya ga sace tarin makamai.
Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani wadanda suka kaddamar da farmakin, wanda bayanai ke cewa ya faru a Mutumji cikin ranakun karshen mako.
Har yanzu Sojin Najeriyar na ci gaba da fatattakar maboyar ‘yan bindigar jihar ta Zamfara matakin da ke zuwa bayan katse layukan sadarwa don magance matsalar da ta addabi jihar da makwabtanta.
Source:BBC
Source:rFi