Akwai wasu halittu da suka saba tunani ko saboda shekaru – kuma suna nan a zahiri.
Za su iya zama haka ko muna tunanin tun asalin halittarsu ba za su mutu ba. Wannan yana nufin, sai idan an kashe su ta hanyar farauta, ko wata cuta ko sauyi na muhallinsu, amma za su iya rayuwa har abada.
Masana kimiyya sun yi kokarin gano sirrin wadannan halittu masu ban mamaki don ganin ko za su iya taimakawa wajen gano alakar tsarinmu na tsufa.
TSUTSAR PLANARIAN
Tun karni na 19 aka fahimci wata nau’in tsutsa ta planarian kan farfado da kanta idan ta rabu biyu.
Amma wannan halittar ta zama ruwan dare a 2012, lokacin da Jami’ar Nottingham ta wallafa wani bincike kan yiyuwar rashin mutuwarta.
Wannan nau’in tsutsa, ana samun ta a sassan duniya kuma akwai nau’ukanta 12 a Birtaniya.
Nau’in tsutsar yana da karfin kwayoyin halitta da ba ya da iyaka na sake farfadowa.
Tsutsar Planarian za ta iya raba kanta biyu ta sake gina kanta
Akwai nau’i biyu na irin wannan tsutsar: Wasu suna hayayyafa ne ta hanyar jima’i wasu kuma ta hanyar rabuwa biyu.
Masana kimiya na Jami’ar Nottingham sun yi nazari kan duka nau’ukan biyu kuma sun gano cewa wadanda ke rabuwa biyu suna iya farfadowa.
A wasu lokuta na rayuwarmu, kwayoyin halittarmu na DNA kamar yawancin dabbobi sukan kai makura na rarrabuwa kuma jikinmu zai fara lalacewa.
Tsutsar planarian kuma a daya bangaren sukan samu karuwar sinadaran jiki da ake kira enzyme da ke kare kwayoyinsu daga tsufa, wanda masana kimiya suka yi imanin cewa ba za su iya mutuwa ba.
TSUTSAR HYDRA
Wannan wata halittar ruwa ce da ke da kamboli a baki.
Hydra na cikin cikin halittun da masanin kimiya na Netherland, Ban Leeuwenhoek, wanda ya samar da na’urar gani ta microscope da gilashi daya mai girma ya yi nazari a kai.
Ba da dadewa ba binciken masanin kimiya na Switzerland Abraham Trembley kan tutsar hydra da karfin farfadowarta ya samar da sabon zamani na fannin ilimin nazarin halittu, a cewar BBC Hausa.
Haka kuma, tsutsotsin hydra suna da karfin iya farfado da sassan jikinsu.
Kuma karfin yiyuwar kasancewar wadanda ba su mutuwa ya dogara ne da kwayoyin halittarsu.
Masanan da suka yi nazari tsawon shekaru kan nau’in hydra sun kasa gano wata alama ta tsufa a tattare da su.
A 2018, masu bincike daga UC Dabis sun yi wani hasashe cewa tsutsar hydra za su iya zama halittar da ba ta mutuwa saboda irin karfin sarrafa kwayoyin halittar da ake kira ‘transposon, wani nau’in kwayar halittar da ke tsalle.
Lokacin da muna da kuriciya jikinmu kan iya sarrafa wadannanwayoyin halittar, amma yayin da muke tsufa za mu fuskanci kalubale.
Source LEADERSHIPHAUSA