Ranar 12 ga disambar kowacce shekara ne almajiran Sheikh Ibrahim Zakazaky suke jaddada tunawa da ranar da suke kira da “Waqi’ar Buhari” wacce suka ce an kashe fiye da mutane 1000 a gidan malamin su dake unguwar gyallesu a zariya.
Rahotanni daga sassa daban daban sun iso hannun jaridar Nigeria21.com wadanda suke nuni da cewa a gobe litinin ne wnad yayi dai dai da 12 ga disamban shekarar 2022 almajiran Sheikh Zakzaky wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a zasu gudanar da tarukan tunawa d kisan kiyashin zariya.
A tattaunawar mu da wani da daga cikin almajiran Malam Zakzaky wanda ya bayyana mana cewa ya halarci unguwar ta gyallesu a lokacin da sojojin Najeriya suke gudanar da kisan kiyashin ya bayyana mana yadda ya shaidi lamarin.
Almajirin MalaM Zakzaky ya bayana mana cewa bai taba ganin rashin imani irin na wannan ranar ba a rayuwar sa.
“Na ga an kashe kananan yara, mata, tsofaffi har ma da jarirai, wasu ma an kone su ne da wuta” a cewar almajirin Malama Zakzaky.
Amma sai dai tun a wannan lokaci da da waqi’ar buhari ta wakana sojojin sun zargi ‘yan shi’a da tare hanyar babban hafsan sojin Najeriya, Janaral Tukur Buratai zargin da almajiran Malam Zakzaky suka karya ta.
Daga cikin hujjojin da almajiran Malam Zakzaky suka bayar dangane da karyata ikirarin sojoji shine, idan an tarewa babban hafsan soji hanya a husainiyya ne to menene ya kai sojojin gyallesu, darur rahma da kuma jushi inda aka binne mahaifiyar Sheikh Zakzaky?
Wannan a ta bakin ‘yan shi’ar na cikin tambayoyin da har zuwa yau sojoji bata amsa musu ba.
Shekarar 2022 na zaman jajiberin shekarar da ake sa ran gwamnatin buhari wacce a lokacin ta ne aka rutsa da ‘yan shi’an zata bar gidan gwamnati, kuma a gobe ne 12 disambar shekarar inda ‘yan shi’a zasuyi tarukan tunawa da bakar ranar a tarihin su.