Alkahira (IQNA) Dar Al-Ifta na kasar Masar ya sanar da mayar da martani ga zaben raba gardama cewa bai halatta a sanya wa wani masallaci sunan masallacin Al-Aqsa ba.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-kahira 24 cewa, masu amfani da dandalin Dar Al-Ifta Masr sun gabatar da tambayar cewa wasu gungun mutane sun gina wani sabon masallaci a wani kauye na kasar da ba na larabawa ba tare da sanyawa masallacin suna masallacin Al-Aqsa.
Jama’a sun yi sabani game da wannan suna, menene hukuncin shari’a a kan haka?
Dangane da wannan tambaya, Darul-Afta na kasar Masar ya sake buga fatawar da ta gabata ta wannan cibiya a shafinta na yanar gizo inda ta rubuta cewa: Masallacin Al-Aqsa na daya daga cikin masallatai da ke da siffofi da siffofi na shari’ar Musulunci.
Wadannan masallatai Allah Ta’ala ya karrama su da kuma tsarkake su.
Sannan kuma ya ruwaito hadisin da aka jinginawa Manzon Allah (SAW) kamar yadda aka karbo daga Musnad Ahmad.
Darul Ifta na kasar Masar ya jaddada cewa: Dangane da haka, sanya sunan duk wani masallaci a doron kasa a matsayin masallacin Aqsa bai halatta a mahangar shari’a ba, kuma Allah madaukakin sarki ne mafi sani a cikin wannan lamari.
Source: IQNAHAUSA