Gwamnatin tarayya ta sanar da majalisar dattawa cewa ta shirya kammala ayyukan layikan dogo amma zata karbo basuka daga kasashen Chana, Fotugal da Turkiyya.
Kamar yadda ministan sufuri, Muazu Sambo ya bayyana, layikan dogon na bukatar kudi masu kauri wadanda za a samo su daga kasashen uku.
Ya sanar da cewa, akwai bukatar kammala wasu ayyukan more rayuwar a wasu sassan kasar nan ta inda layikan dogon zasu ratsa a kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta sanar da majalisar tarayy cewa tana fatan kammala ayyukan layin dogo da ake yi a fadin kasar nan na biliyoyin dalolin basussukan da zata samu karbowa daga China, Fotugal da Turkiyya.
Kamar yadda gwamnatin tarayya tace, ta mayar da hankali wurin tabbatar da ayyukan titunan jiragen kasan Najeriya na zamani, jaridar Vanguard ta rahoto.
A yayin jawabi a ranar Alhamis a Abuja yayin da ya bayyana gaban kwamitin hadin guiwa na majalisar tarayya kan sufurin tudu da ruwa, wanda ya samu shugabancin Sanata Danjuma Goje na jam’iyyar APC daga Gombe ta tsakiya, ministan sufuri, Muazu.
Jaji Sambo yace cike da nasara ake fadada layikan dogon ta hanyar amfani da kudaden da ake warewa ma’aikatar tunda gwamnatin tarayya tana fuskantar kalubale wurin samun bashi.
Sambo yace: “A halin yanzu ana aikin zamanantar da layikan dogo na Kaduna zuwa Kano, Fatakwal zuwa Maiduguri da Kano zuwa Maradi da kudin da aka fitar na 2022. “
Ma’aikatar tana fatan ma’aikatar kudi ta kammala sasancin Karbo bashi domin cigaban wadannan ababen more rayuwar daga Chana, Fotugal da Turkiyya.
“Domin tabbatar da kammala tare da sa hannu kan yarjejeniyar, shaidar inda aka samo karin kudin aikin da na sauran bangarorin aikin da za a biya kai tsaye daga gwamnatin tarayya an bai wa wadannan cibiyoyin kudin ta hanyar isasshen kasafi a shekarar 2023 da kasafi na gaba.”
Ministan yayi bayanin cewa, sashin Legas zuwa Ibadan na aikin Legas zuwa Kano da Itakpe zuwa Warri na lagin dogon duk yanzu suna aiki kuma jama’a na jin dadinsu.
Ya kara da cewa domin tabbatar da kammaluwar ayyukan, wasu ayyukan da suka hada da kammala gadar sama, hada wutar da rum in Wutar Lantarkin kasa da sauransu dole ne su kammalu.
Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari.
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kare gwamnatinsa kan hukuncinta na karbo basussuka daga China, ya ce duk wanda zai taimaka wurin samarwa da Najeriya ababen more rayuwa ana maraba da shi.
Kamar yadda bayanin da Ofishin kula da basussuka ya sanar, Najeriya ta aro $2.02 biliyan a matsayin bashi daga China daga 2015 kuma bashin kasar nan ya kai $3.40 biliyan daga China a ranar 31 ga watan Maris na shekarar da ta gabata.
Source:legithausang