Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira, ta ce tana nazari a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, inda ta ce za ta sanar da hukuncin da ta yanke a cikin wata mai kamawa.
Magoya bayan tsohuwar ministar shari’ar dai sun shafe watanni suna ta kira da ta fito takara don kasancewa shugaban Faransa bakar fata ta farko, da zummar dakile habakar da masu zazzafan ra’ayi ke yi.
A shekarar 2013 ne dai Taubira ta gabatar da batun auren jinsi, lamarin da ya janyo zanga- zanga da mahawara a majalisar dokokin Faransa, a lokacin da take matsayin ministar shari’a, a karkashin mulkin tsohon shugaba François Hollande.
Ta kuma yi fice a matsayin wadda ta jagoranci bukatar bijiro da dokar nan da ta ayyana cinikin bayi a matsayin laifin cin zarafin dan Adam a shekarar 2001.
Taubira, ta fito ne daga yankin Cayenne na jihar Guiana ta Faransa, kuma ta samu yabo daga masu sassaucin ra’ayi saboda kwarjininta a majalisar dokoki, da mahawarar da take yi a talabijin.
Ta tsaya takarar shugabancin Faransa shekaru 20 da suka wuce, inda ta samu nasarar lashe kaso 2 na kuri’un da aka kada a zagaye na farko a zaben.
A wani labarin na daban kasar Rasha ta gabatar da bukatun ta ga Amurka da kungiyar tsaro ta NATO kan rikicinta da kasar Ukraine, tare da yi na kira da a gudanar da tattaunawar gaggawa da fadar White House a daidai lokacin da rikici tsakanin Rashan da manyan kasashen yammacin Turai ke kara ta’azzara a kan kasar ta Ukraine.
A wani taron manema labarai, bayan fitar da daftarin, mataimakin ministan harkokin waje Sergei Ryabkov, ya ce Rasha a shirye take ta kan harkar tsaro da Amurka .
Fitar da wannan daftari dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsamin alaka ke kara tsananta tsakanin Rasha da kasashen Yammancin Turai kan rikicin Ukraine.
Kasashen dai na zargin Rasha da shirya kai farmaki kan Ukraine, suna masu ikirarin cewa shi babban dalilinta na jibge dubban sojoji a kan iyakokin kasar.