‘Yan sandan Jamaica sun cafke wani tsohon dan majalisar dokokin kasar Haiti da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa shugaban kasa.
Majiyar ta ce ‘yan sandan Jamaica sun yi aiki ne tare da takwarorinsu na kasa da kasa kafin cafke tsohon dan majalisar.
An kashe tsohon shugaba Moise ne tare da jikkata matarsa da munanan raunuka a lokacin da gungun makasa kusan 20 suka kutsa cikin gidan shugaban kasar na Haiti tare da bude musu wuta.
A wani labarin mai kama da wannan Babban mai shigar da kara na Haiti ya mika bukatar fara tuhumar Firaministan kasar Ariel Henry dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise.
Hujjoji na ci gaba da karfafa wadanda ke zargin hannun Firaministan a kisan shugaba Jovenel Moise yayin wani farmaki da mahara suka kai gidansa watanni kusan 3 da suka gabata.
Cikin wata wasika wadda ke matsayin ta 2 da sashen shigar da karar ya gabatarwa gwamnati ya nemi hukumar shige da fice ta kasar ta haramtawa Firaminista Ariel Henry barin kasar a kowanne yanayi.
Wata shaidar baya-bayan nan ta nuna yadda Henry ya yi waya da babban wanda ake zargi da kisan shugaban na Haiti, lokaci kankani bayan farmakin da ya hallaka shugaban.
Wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara ta kasar ta kuma nemi izinin gurfanar da Firaministan don amsa tuhuma dangane da alakarsa da maharan na ranar 6 ga watan Yuli.
Tun a juma’ar da ta gabata babban mai shigar da karar ya aikewa da Firaministan bukatar ganin ya bayyana gaban kotu jiya talata don amsa tambayoyi da ke matsayin kari kan bayyanarsa gaban mahukuntan kasar sa’o’I kalilan bayan kisan shugaba Moise amma kuma yaki mutunta gayyatar.