Wani rahoton MDD ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na farfadowa da karfinsa bayan annobar COVID-19, inda yake kara bayar da kwarin gwiwa game da makomarsa.
A ranar Talata ne MDD ta fitar da sabon rahoto na tsakiyar shekara, kan yanayin tattaliin arzikin duniya da kuma makomarsa a 2023, wanda ya yi hasashen tattatlin arzikin Sin zai karu da kaso 5.3 a bana, wanda ya dara kaso 4.8 da aka yi hasashe a watan Janairu.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Hamid Rashi, wanda shi ne shugaban reshen dake bibiyar yanayin arzikin duniya da manufofin tattalin arziki na sashen kula da tattalin arziki da harkokin jama’a na MDD, wanda kuma shi ya jagoranci hada rahoton, ya ce wani abu da ya tallafa yayin sake nazartar hasashen tattalin arzikin Sin shi ne, farfadowa mai karfi da bangaren sayar da kayayyaki dai-dai ya yi, wanda ya nuna karuwar bukatu a tsakanin iyalai.
Ya kara da cewa, wasu abubuwa biyu kuma su ne, kasuwar hada-hadar gidaje ta kasar Sin ta daidaita sosai, kuma ba kamar a sauran kasashe masu karfin arziki ba, kasar Sin ta na da muhimman dabarun kasafi da na kudi, domin taimakawa shirye-shiryen raya tattalin arziki.
A cewarsa, tattalin arzikin kasar Sin na kan tubali mai kwari idan aka kwatanta da na sauran kasashe, duk da wasu barazana dake akwai.(Faeza Mustapha.