Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta ce tashin farashin kayan masarufi a Nijeriya ya kai kashi 31.70 cikin ɗari a watan Fabrairu.
Wannan na nuni da kari daga alkaluman baya na kashi 29.90 idan aka kwatanta da bara, daidai watan Fabrairu inda aka samu karin kashi 9.79.
Alkaluman NBS sun nuna yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya ya fi tsadar abinci, inda a Arewa maso Yamma aka fi samun rangwame.
Mai taimaka wa shugaba Tinubu kan labarai,Abdul’aziz Abdul’aziz, ya ce don magance kunci ne ya sa shugaban ganawa da shugabannin kasashe masu arziki don zuba jari a Nijeriya.
Tun bayan cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayun 2023 aka shiga tsadar rayuwa a Nijeriya.
Tsadar rayuwar dai ta haifar da zanga-zanga a wasu sassan Nigeria, sai dai Tinubu ya yi burus da koken da mutane suka yi, inda ya ce ba gudu ba ja da baya game da batun cire tallafin man fetur.
A wani labarin na daban matashin dan wasan tsakiya dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Amad Diallo, ya bayyana cewar da azumi a bakinsa a lokacin da ya jefa kwallon da ta yi sanadiyar tsallakawar Manchester United zuwa matakin kusa da na karshe na gasar FA Cup.
Diallo wanda ya canji Raphael Varane a minti na 85 ya shigo da kafar dama, inda ya taimakawa Manchester United wajen tsallakawa zuwa matakin kusa da na karshe a mintunan karshe na wasan.
Bayan kammala mintuna 90 na wasan ba tare da wata kungiya ta samu nasara ba, alkalin wasa John Brooks ya kara mintuna 30 inda Harvey Elliott da Marcus Rashford kowa ya jefa kwallo daya.
DUBA NAN: Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Samar Da Rufe Makarantu Saboda Tsananin Zafi
Kwallon da Diallo dan asalin kasar Cote de’Voire ya zura a minti na 120 yasa Manchester United ta tsallaka zuwa matakin wasan kusa da na karshe na gasar FA, inda zata hadu da Coventry City.